✕ CLOSE Noma Da Kiwo Hotuna Kiwon Lafiya Girke-Girke Sana'o'i Kimiyya da Kere-Kere Ra'ayin Aminiya Ra’ayoyi Rahoto
Click Here To Listen To Trust Radio Live

Mutuwa rigar kowa (1)

A kullum na ci karo da mutuwa kowace iri ce abubuwa da dama ke zuwa mini a rai, amma mafi damuwa a gare ni shi ne…

A kullum na ci karo da mutuwa kowace iri ce abubuwa da dama ke zuwa mini a rai, amma mafi damuwa a gare ni shi ne yadda a yawancin lokuta mutuwa ba ta kasancewa darasi ga yawancin mutane. A yi ta yau, gobe an manta. A yi ta jibi, gata an manta. Bare kuma wadda aka yi shekarar nan zuwa badi, ba a ko zancenta, bare a tuna, sai wata ta sake sadadowa, sai a hankalta zuwa gobe an sake mantawa.

Wannan ne ya sa ko da na yi rashin babban abokina, Farfesa Aminu Isiyaku ’Yandaki a makon jiya, wannan ne ya sake fado mini a rai, kuma darussan mutuwar su suka sake firtso min, ta yadda na kara tabbatar da abubuwan da mutuwa ce kadai ke samar da su.

Lallai mutuwa karar kwana ce, domin kuwa, kowa da adadin kwanakin da aka yi masa a doron kasa. Ke nan muna iya cewa mutuwa riga ce da kowa da kowa zai sa komai matsayi ko iko. Wannan ne ya sanya mutuwa ta kasance wa’adi da kowa ke jirans. Saboda haka muna iya cewa mutuwa ka’ida ce da kowa sai ya cika, matukar an hura masa rai.

Bisa irin wannan tunani ne wadansu ke ganin mutuwa hutu ce ga kowane mamaci, musamman idan aka yi la’akari da kujuba-kujubar da mutane ke fama da su na rayuwa kafin tafiya. Ke nan ita kanta mutuwa balaguro ce da dole kowa sai ya yi tattaki domin isa ga wani matsuguni. Matsuguni kuwa ga dan Adam matuka ne, tamkar mutuwa wadda ta kasance karshe ce, matabbata ce ga kowane mahaluki.

Duk da wannan fasalce-fasalcen mutuwa da yawan yanaye-yanayenta muna iya karawa da cewa mutuwa tonon asiri ce, tun ba a isa ga madakata ba. Wadannan bayanai ina tsammanin ba sa bukatar karin haske ko jaddadawa, domin sun faru, suna faruwa, kuma za su ci gaba da faruwa har ranar kashe mutuwa ita kanta. Sai dai abin da ke da muhimmanci ga kowane dan Adam shi ne ya fahimci sirrin da ke tattare da mutuwa da kuma tonon sililin da take yi wa rayuwa kafin ta wuce. Ta haka ne nake zaton za mu kara nakaltar rayuwar da muke ciki, kafin mutuwa ta yi mana sallama.

Abin da ya dace mu soma da shi a nan bai wuce kokarin fahimtar me ya sa ita rayuwa take kasancewa a bisa faifai a koyaushe ba, amma kuma mu kasa fahimtar abin da ta bayyanar har sai mutuwa ta bayyanar, ta tona asirin duk wanda ta cimma a cikin zangon tafiye-tafiye na yau da kullum? Me ya sa duk da cewa hadarin rayuwa yana kulluwa ne a gabanmu, amma kuma sai ya zo ya iske mu ba mu shirya wa ambaliyar ruwan saman da hadarin zai antayo da shi ba? Mu ne da kame-kame da guje-guje da neman mafita a lokacin da komai ya jagule, ya rikirkice har sai ruwan ya yi mana dukan tsiya! Me ya sa duk da cewa tufafin rayuwa farare suke, amma mu kare da kazancewa a lokacin da mutuwa ta zo, mu zamanto cikin dauda, kayayyakin namu su yi baki, kirin? Me ya sa muke barin mutuwa na tona mana asiri, alhali muna iya rufe asiran cikin kwando ko wani abu makamancin haka?

Sai dai ina son a kula da wani abu, ni ba tonon asirin da mutuwar ke yi wa mamata ba ne ke damuna, illa irin yadda muke mance abubuwan da rayuwar ta tanada kafin a kai makabarta. Abubuwan da na gani ko na ji game da wannan matsala suna da yawa, amma zan fi mayar da hankali kan biyu ko uku a wannan karo.

Na farko tun muna kanana na sha nazarin yadda mutuwa ke zuwa afujajan a cikin al’ummarmu da yadda muke kallon irin ‘barnar’ da take yi mana, amma ba wai na tono asiri ko na silili ba. Lallai mun san za a mutu, amma mamata ba sa kasancewa cikin takura ko matsi na yanayin da hakan ya faru gare su. Haka kuma wadanda aka bari a baya, su ma ba sa shiga cikin kunci da rayuwar ni’yasu, domin kuwa kafin a kai ga kushewar an tanadi abubuwan da suke muhimmai dangane da rage wa mai niyya zuwa madakata, domin ya tafi cikin kwanciyar hankali da godiya, domin Allah Ya sanya yana tare da ’yan uwa da abokan arzikin da sun yi iya kokarinsu don agazawa, amma da yake mutuwa tamkar barci ce, barauniya ce, sata take yi, dole a tafi, ko da ba a shirya ba, ya sa ba mai kukan tonon asiri ko damuwa da yadda gaba za ta kasance.

Shi ya sa a wancan lokaci, yara kanana irinmu, har murna muke yi idan an yi kira da a matso zuwa ga makara, duk da cewa ba a bari mu kai gare ta, bare mu taba ko mu kama wajen dauka, duk da haka da zarar makara ta shiga kuryar masallaci bayan an dawo rakiyar masu zuwa kushewa, dadi da annashuwa ke biyo baya ga yara. Abinci dai ba abin damuwa ba ne, abin sha da ma akwai a wajen makwabta da iyalan mamata. Abin da ya kasance kari shi ne kwabban sadaka da yara ke kwasa daga hannun mutanen unguwa domin a isar da ladar ga mamaci. A wancan lokaci ba mai damuwa da matsaloli ko tunanin yaya za a yi da ’ya’yan da aka bari. Wa zai dauki dawainiyar karatu da ci da su da makwancinsu da sauran al’amurran yau da kullum, domin kuwa al’umma ce guda, tamkar tsintsiya. Ke nan da wuya a ce an yi rashi. Eh, an yi rashi kam na mamaci, domin ba za a sake ganinsa yadda aka saba a cikin gida ko bakin garka ko masallaci ba, amma iyalan mamata sun san ba su yi rashin abubuwan rayuwa ba, domin an tanadi abubuwan da za su agaza musu, wasu ma tanadin na har abada ne.

A wancan lokaci ne ake maganar agola, idan mahaifiya ta sake aure, ’ya’yan su kasance tamkar ’ya’yan sabon maigidan da suka samu kansu a ciki. In kuma wata mutuwar ta ratsa, dorawa kurum za a yi, tsoffaffin agola su sake komawa sababbin agola a wani gidan, su kuma sababbin agola, su samu sabon matsuguni ko a wani sabon gida ko a tsakanin kawunnai da goggoni da innoni da babanni. Wadansu yaran ma ba su iya tuna rashin da suka yi, in ba na zahirin rashin ganin iyayensu ba. Rayuwa tafiya take kamar ba a samu tuntube ba. Yanzu fa? Abubuwan tuni sun cana!