✕ CLOSE Noma Da Kiwo Hotuna Kiwon Lafiya Girke-Girke Sana'o'i Kimiyya da Kere-Kere Ra'ayin Aminiya Ra’ayoyi Rahoto
Click Here To Listen To Trust Radio Live

Mutuwar dan kwallo: Za a rika hukunta shugabannin wasanni –Dare

NFF ta dakatar da gasar Firimiya   Ma’aikatar Matasa da Wasannin ta Kasa ta ce za ta fara daukar matakan hukunta shugabannin kowane wasan kwallon…

  • NFF ta dakatar da gasar Firimiya

 

Ma’aikatar Matasa da Wasannin ta Kasa ta ce za ta fara daukar matakan hukunta shugabannin kowane wasan kwallon kafa na rukuni-rukuni na kasa wadanda ba su samar da ingantattu da wadatattun kayayyakin agaji ga ’yan wasan a filin wasanninsu ba. Ministan Matasa da Wasanni, Mista Sunday Dare ne ya sanar da haka a wata wasikar ta’aziyya da ya aike wa Gwamnatin Jihar Nasarawa da Hukumar Kungiyar Kwallon Kafa ta Nasarawa United da iyalan wani dan wasan kungiyar da ke tsaron baya mai suna Chineme Martins wanda ya yanke jiki ya fadi ya mutu nan take lokacin da kungiyar ke buga wasanta na rukuni-rukunin da kungiyar Katsina United a filin wasa na Lafiya a ranar Asabar da ta gabata.

A wasikar ta’aziyyar wanda Ministan ya tura wadda wakilinmu ya samu kwafi, ya bayyana takaicinsa a madadin Ma’aikatar Wasanni ta Kasa dangane da abin da ya bayyana da sakaci kan yadda a cewarsa rahotannin da ya samu sun nuna babu kayayyakin agajin gaggawa ga ’yan wasan da sauran kayayyakin kariya a lokacin wasan.

Ya ce a kan haka ne ya sa ma’aikatar ta yi wani zaman gaggawa inda ta umarci wadansu jami’anta su rika ziyartar filayen wasannin kwallon kafa da sauran wasanni a duk lokaci da ake wasa don sa-ido kan ire-iren kayayyakin agaji da likitocin da ke kula da lafiyar ’yan wasan da sauransu.

Haka ya ce za a hukunta shugabannin da suka shirya duk wasan da aka gano da laifin karancin kayayyakin agaji. Ya kalubalanci gwamnatocin jihohin kasar nan kan su rika tallafa wa fannin wasanni a jihohinsu musamman da wadannan kayayyakin agaji don guje wa sake aukuwar irin wannan lamari nan gaba.

Daga nan ya yi ta;aziyya ga iyalan dan wasan inda ya nemi su dauki lamarin a matsayin kaddara daga Ubangiji wadda ka iya faruwa da kowa a kowane lokaci.

A bangare Gwamnatin Jihar Nasarawa ta ce za ta samar wa fannonin wasanninta isassun kayayyakin agaji da kariya musamman fannin wasan kwallon kafa a dukkan matakai. Gwamnan Jihar Injiniya Abdullahi Sule ne ya bayyana haka ga manema labarai jim kadan da aukuwar wannan lamari.

Gwamnan wanda ya kalli wasan tare da Sakataren Gwamnatin jihar da wadansu manyan mukarrabansa a ranar har lokacin da dan wasan ya gamu da ajalinsa, ya ce ba shakka hakan wata manuniya ce ga gwamnatinsa kan ta inganta wadannan kayayyakin agaji na gaggawa a jihar don kauce wa sake aukuwar lamarin nan gaba.

Ya ce ba shakka an samu matsala a fannin masu kula da ’yan wasan na ko-ta-kwana da kuma kayayyakin agajin inda ya ce gwamnatinsa ba tare da bata lokaci ba za ta samar da ingantattu kuma isassun kayayyakin.

Ya bayyana tausayinsa ga iyalan dan wasan inda ya yi alkawarin tabbatar da cewa gwamnatinsa ta tallafa musu musamman ’ya’yan mamacin.

Binciken wakilinmu ya gano cewa marigayi Chineme Martins ana kan buga wasan ne kawai aka ga ya yanke jiki ya fadi a kusan karshen wasan inda duk kokari da likitocin da ke a filin wasan suka yi don farfado da shi ya ci tura kafin daga bisani a kai shi Asibitin Kwararru na Dalhatu Araf da ke Lafiya inda aka tabbatar da rasuwarsa.

Wakilinmu ya tuntubi babban likita kuma Shugaban Asibitin Kwararru na Dalhatu Araf, Dokta Hassan Ikrama ta wayar tarho don jin ta bakinsa dangane da lamarin inda ya ce ana shigowa da dan wasan asibitin aka fara gwaje-kwaje a kansa amma sai aka tarar a mace yake kasancewa a cewarsa an makara wajen isowa da shi asibitin.

Ya bayyana takaicinsa dangane da rashin isassun kayayyakin agaji a filayen wasannin jihar da wasu na sassan kasar nan inda ya bukaci wadanda hakkin haka ya rataya a wuyansu su tabbatar sun magance lamarin cikin gaggawa.

Kafin aukuwar lamarin Kungiyar Nasarawa United tana cin takwararta ta Katsina United da ci 3 -0 kuma har zuwa lokacin da ake hada wannan rahoto babu wani jawabi a hukumance da ya fito daga Kungiyar Nasarawa United.

Haka kuma a wata sanarwa Hukumar Wasan Kwallo ta Kasa (NFF) ta dakatar da ci gaba da gudanar da gasar Firimiya ta kasa ta bana saboda rasuwar dan wasan kungiyar ta Nasarawa United, Chineme Martins, har zuwa lokacin da aka tabbatar kungiyoyin kwallon kafa da hukumomi sun yi kyakkyawan tanadi na kayan agajin gaggawa a  filayen wasanni da ake gudanar da gasar Firimiya.