✕ CLOSE Noma Da Kiwo Hotuna Kiwon Lafiya Girke-Girke Sana'o'i Kimiyya da Kere-Kere Ra'ayin Aminiya Ra’ayoyi Rahoto
Click Here To Listen To Trust Radio Live

N-Power: An kama mai damfarar ‘yan gudun hijira

Jami’an tsaro sun damke wani mutum da ke damfarar ‘yan gudun hijira yana sayar musu fom din daukar aikin N-Power a kan Naira dubu biyar-biyar.…

Jami’an tsaro sun damke wani mutum da ke damfarar ‘yan gudun hijira yana sayar musu fom din daukar aikin N-Power a kan Naira dubu biyar-biyar.

‘Yan gudun hijra sama da 40 ne suka fada tarkon mazambacin kafin dubunsa ta cika jami’an tsaron farin kaya na NSCDC su cika hannu da shi a Karamar Hukumar Guzamala ta jihar Borno.

Daya daga cikin ‘yan gudun hijirar da aka damfara, Musa Ali, ya shaida wa Aminiya cewar shi da abokansa sun biya mutumin kudin fom din Naira dubu biyar-biyar.

Ya ce bayan dan dafarar ya karbe kudadensu kusan N100,000 suka tuntubi shugaban sansanin ‘yan gudun hijira na Bakassi, wanda ya wayar musu da kai cewa kyauta ake cike fom din kuma an damfare su.

Musa ya ce, hakan ya sa suka yi wa mutumin dubarar cewa wasu za su kara sayen fom din na N-Power, “Zuwansa ke da wuya jami’an tsaro suka yi caraf ta shi”.

Shugabannin sansanin  ‘yan gudun hijira na Bakassi sun tabbatar da aukuwar al’amarin, yayin da mai magana da yawun NSCDC, James Bulus ya ce mutumin yana hannunsu suna bincikar sa kan laifin damfarar ‘yan gudun hijirar