✕ CLOSE Noma Da Kiwo Hotuna Kiwon Lafiya Girke-Girke Sana'o'i Kimiyya da Kere-Kere Ra'ayin Aminiya Ra’ayoyi Rahoto
Click Here To Listen To Trust Radio Live

Na bar fim saboda zai raba ni da Musulunci – Zaira Wasim

Jarumar Fina-Finan Indiya (Bollywood) Zaira Wasim mai shekara 18 a duniya ta bayyana cewa za ta yi adabo da harkar fim saboda abin da ta…

Jarumar Fina-Finan Indiya (Bollywood) Zaira Wasim mai shekara 18 a duniya ta bayyana cewa za ta yi adabo da harkar fim saboda abin da ta kira ‘barazanar’ da sana’ar fim din ke haifarwa ga sha’anin addini.                                                                                                                                                  An ruwaito jarumar tana cewa: “Tafiya ce mai matukar wuyar sha’ani; da na share lokaci mai tsawo ina yakar ruhina.” Kamar yadda ta rubuta a wani rubutu mai tsawon gaske a shafinta na Facebook, a ranar Lahadin da ta gabata.

Indiyawa sun yi ta mayar da martani game da  labarin nata; inda da dama suka yi ta sukar dalilin nata na barin harkar fina-finan.

Misis Wasim dai tauraronta a harkar fina-finan na Bollywood ya fara haskawa ne a shekarar 2016- lokacin da ta fito a wani fim mai suna Dangal, daya daga cikin fina-finan Indiya da suka yi tashe a baya-bayan nan.

Jarumar-wacce ’yar yankin Kashmir da Indiya ke iko da shi ne; a shafinta na Facebook, ta yi karin haske game da yadda ta sha gwagwarmaya a masana’antar fina-finan, da kuma yadda hakan ya shafi dangantakarta da addininta na Musulunci.

Abin da ta wallafa a shafin sada zumuntar, tuni ya yadu inda ya yi ta samun dubban sharhi da nuna so.

“A lokacin da na fara fahimta tare da yin nazarin abin da na sadaukar da lokacina a kai; tunani da hankalina sun nuna min cewa, lokaci ya yi da zan bude wani sabon babin rayuwa; kawai sai na ji cewa, eh lallai na dace sosai da masana’antar; amma dai ba wurin zamana ba ne,” kamar dai yadda ta wallafa.

Ta kara da cewa: “Sana’ar fim, ta gadar min da soyayya da kauna da goyon bayan jama’a da ma yarda daga jama’ar; sai dai a daya bangaren ta kuma dulmiyar da ni zuwa ga jahiltar addini, ta yadda sannu a hankali ba tare da na farga ba; ta nesanta ni da addinin Musulunci. A lokacin da na ci gaba da kasancewa cikin sana’ar da a kullum take yin katsalanda a harkar addinina; to kuma lallai hakan zai yi ta yin barzana ga addinin.”

Ta ci gaba da cewa, a kullum sana’ar na jefa ta cikin ‘raunin imani.’ “Abu ne mai saukin gaske, kullum in tsinci kaina a yanayin da zai bata mini kwanciyar hankali da imanina da ma dangantakata da Mahaliccina.”

Matakin da jarumar ta dauka, ya haifar da zazzafar muhawara a shafin Twitter, inda mutane da dama suka  kalubalanci dalilin ‘addini’ a matsayin hujjar yin adabo da harkar fim da ta yi.

Sai dai kuma, akwai wadansu da suka yi ta kare matakin nata, ciki har da Omar Abdullah, tsohon Ministan Lardin Jammu da Kashmir.

Fim dinta da zai fito nan gaba, shi ne ‘The Sky Is Pink’ zai kasance fim dinta na karshe. A cikin fim din, jarumar nan Priyanka ta fito; kuma an tsara fitowarsa wani lokaci cikin shekarar nan.