Subscribe
  • facebook
  • twitter
  • whatsapp
  • linkedin
‘Na dauki Buhari a matsayin uba’

Godwin Obaseki, Gwamnan Jihar Edo

‘Na dauki Buhari a matsayin uba’

Gwamna Godwin Obaseki na Jihar Edo ya ce dangantakar da ke tsakaninsa da Shugaban KasaMuhammadu Buhari ta da da uba ce.

Obaseki, jim kadan bayan tattaunawarsu da Buhari ta bidiyo, ya ce sun yi magana ne kan abubuwan da suka shafi cigaban al’mmar Edo ne da kuma hanyoyin magance matsalolin annobar COVID-19.

“Dangantaka ta da Shugaban Buhari ta da da uba ce. Mun tattauna da shi ta kafar zoom. Mun kuma tattauna a kan matsalolin da suka shafi al’ummar Edo da ‘yan Najeriy da kuma hanyoyin magance yaduwar cutar coronavirus”, inji Obaseki a shafinsa na Facebook.

Jawabin nasa ya zo ne akalla watanni biyu kafin a gudanar da zaben gwamnan jihar wadda za a yi a ranar 19 ga watan Satumba, 2020.