Da Dumi Dumi

Na dawo daga rakiyar shan Gahawa – Salman Klhan

A kwanan nan ne dan fim din Indiya da tauraruwarsa ke haske, Salman Khan ya bayyana niyyarsa ta daina shan gahawa.
Mutane da yawa da ke bibiyar halayyar dan wasan, sun yi mamakisa da ya dauki wannan mataki, musamman ganin cewa ya saba da wannan dabi’a ta shan gahawa a duk lokacin da ake daukar fim tare da shi. Haka kuma sun yi la’akari da yadda ba da dadewa ba Salman ya daina shan giya kuma ya yi hannun riga da shan sigari.
A yayin da Salman ya yi adawa da gahawa, wata majiya ta ce ya koma shan ‘Koren Shayi.’ Kamar yadda ya ce, wannan shayi yana da sinadarai da ke bunkasa lafiya. “Dalili ke nan a yanzu za ka ga dan wasan yana tsotsar sabon shayin nasa a duk lokacin da yake aikin daukar fim, da dare ko da rana.” Inji wata majiya.
Da ake bayyana dalilinsa na daukar wannan mataki na daina shan taba da giya da gahawa, wata majiya ta kusa da shi ta bayyana cewa ya dauki matakin ne da nufin kare lafiyarsa, kasancewar yana fama da wata cuta da ke sanya masa zafi a kumatu. Cutar da ta tilasta aka yi masa hida a Satumbar 2011, a wani asibitin birnin Los Angeles da ke Amurka.

Share