✕ CLOSE Noma Da Kiwo Hotuna Kiwon Lafiya Girke-Girke Sana'o'i Kimiyya da Kere-Kere Ra'ayin Aminiya Ra’ayoyi Rahoto
Click Here To Listen To Trust Radio Live

Na fara kasuwanci da Naira 38 ne – Shugaban JIFATU

Shugaban Rukunin Kamfanonin JIFATU, wato (JIFATU General Enterprises), Alhaji Sabitu Muhammad Yahaya ya ce ya fara kasuwancinsa ne da Naira 38 kacal shekara talatin da…

Shugaban Rukunin Kamfanonin JIFATU, wato (JIFATU General Enterprises), Alhaji Sabitu Muhammad Yahaya ya ce ya fara kasuwancinsa ne da Naira 38 kacal shekara talatin da biyu da suka gabata.

Alhaji Sabitu Yahaya ya bayyana haka ne lokacin da yake jawabi a rana ta musamman da aka ware ga Kamfanin JIFATU a ci gaba da gudanar da bikin baje kolin da ake yi a Jihar Kano.

Alhaji Sabitu Yahaya ya  ce, “A 1986 na fara harkar kasuwanci inda nake sayar da maganin bera wanda ake kira samandagari wato tarkon bera. Haka nake yawon bin kasuwannin kauyuka kamar su Dandume da Sabuwa da Giwa da sauransu ina tallar tarkon beran.”

Shugaban na JIFATU ya kara da cewa ya kasance yana tafiyar da harkar kasuwancinsa sannu a hankali, ba tare da yin tsallake wasu matakai ba inda ya yi kira ga matasa su daina mafarkin yin arziki dare daya, “Tunda na fara kasuwanci a hankali nake tafiya, mataki zuwa mataki. Ban taba tsalle daga nan in je can ba har sai na jira  Allah Ya kai ni. Ba mu taba cewa sai lallai mun kai wani matakin da ba mu kai ba. Mun yi imani komai lokaci ne. Don haka nake kira ga matasa su daina ci da zuci wajen ganin sun yi arziki dare daya,” inji shi.

Ya ce babu abin da ya kai shi matsayin da yake kai sai jajircewa, “Ita harkar kasuwanci aba ce da take bukatar jajircewa da fata tagari. Lokacin da muka fara manyan shaguna irin na Bature a nan gani ake ba za mu iya ba, amma da yake mun jajirce sai ga shi mun kai inda ake ganinmu a yau,” inji shi.

A cewarsa ba wai a harkar sayar da kayayyaki Kamfanin JIFATU ya tsaya ba, “Tun daga lokacin da Shugaban Kasa Muhamamdu Buhari ya yi kira a koma gona muka dukufa wajen yin noma ka’in-da-na’in. Daga nan kuma sai muka shiga sarrafa kayan amfanin gonarmu ta hanyar inganta su. Misali muna da garin masara da Semobita da garin alkama da tsakin alkama da fulawa da sauransu,” inji shi.