✕ CLOSE Noma Da Kiwo Hotuna Kiwon Lafiya Girke-Girke Sana'o'i Kimiyya da Kere-Kere Ra'ayin Aminiya Ra’ayoyi Rahoto
Click Here To Listen To Trust Radio Live

Na fi ganin kaina dan Arewa fiye da Kudu – Dan Takarar Jam’iyyar  PT

Dan takarar Shugaban kasa a zaben 2019, karkashin Jam’iyyar PT, Cif Gbenga Olawepo Hashim ya bayyana  cewa ya fi ganin kansa a matsayin dan Arewa…

Dan takarar Shugaban kasa a zaben 2019, karkashin Jam’iyyar PT, Cif Gbenga Olawepo Hashim ya bayyana  cewa ya fi ganin kansa a matsayin dan Arewa fiye da mutumin Kudu inda ya fi suna.

Dan takarar wanda ya bayana haka a yayin zantawa da Aminiya a Abuja, ya ce sabanin abin da wadansu ke daukarsa, shi cikakken dan Arewa ne kasancewar mahaifinsa mutumin garin Yawuri ne da ke Jihar Kebbi kuma shi kansa a can a ka haife shi, sannan ya yi karatunsa na farko a yankunan Borgu da Kainji da ke Jihar Neja.

Ya ce kasar nan na bukatar hugaba irinsa da ke da masaniyar bangarorinta don kyautata zamantakewar al’ummarta, kasancewar mahaifinsa daga Arewa yake sannan mahaifiya kuma daga yankin Yarbawa.

Babban Sakataren Yada Labarai na dan takarar, Malam Ibrahim Hassan ya bayyana dan takarar a matsayin mutum mai fafutika a kan hakkokin jama’a tun a lokacin da yake jami’a da kuma lokacin gwagwarmayar kafa dimokuradiyya a kasar nan, inda ya ce hakan ya jawo masa dauri a lokuta daban-daban.

Ya ce idan aka zabi Gbenga Olawepo Hashim a matsayin Shugaban Kasa a zabe na gaba, zai mayar da hankali ga bangaren samar da ayyukan yi da kuma kyautata harkokin tattalin arzikin kasa a matsayin babban mataki na magance rigingimu da kuma ta’addanci. Ya ce dan takarar na Jam’iyyar PT ya taka rawar gani wajen kafa Jam’iyyar PDP a baya, kuma ya rike matsayin Mataimakin Jami’in Watsa Labarai na jam’iyyar a lokacin shugabanta na farko marigayi Solomon Lar.

Da ya juya ga bangaren kwarewarsa, ya ce dan takarar ya karanci aikin jarida ne, inda ya samu digiri na farko a Jami’ar Legas sannan ya fadada karatunsa a wata jami’a da ke Turai. Ya ce dan takarar ya goge a bangaren kasuwanci, kuma a shirye yake ya sadaukar da dukiyarsa don ganin ya samar wa ’yan Najeriya rayuwa mai kyau, ya ce hakan shi ne babban dalilin tsayawarsa takarara a zaben na 2019.