✕ CLOSE Noma Da Kiwo Hotuna Kiwon Lafiya Girke-Girke Sana'o'i Kimiyya da Kere-Kere Ra'ayin Aminiya Ra’ayoyi Rahoto
Click Here To Listen To Trust Radio Live

Na fi son mukamin Minista a kan na Sanata – Akpabio

Ministan Ma’aikatar Raya Yankin Neja-Delta Mista Godswill Akpabio ya zabi ya ci gaba da zama kan kujerar Minista maimakon komawa ya maimaita takarar Sanata daga…

Ministan Ma’aikatar Raya Yankin Neja-Delta Mista Godswill Akpabio ya zabi ya ci gaba da zama kan kujerar Minista maimakon komawa ya maimaita takarar Sanata daga Jihar Akwa Ibom.

Mista Akpabio ya shigar da kara a kotu bayan faduwa a zaben Majalisar Dattawa inda kafin samun hukuncin kotu, Shugaba Buhari ya nada shi Minista Ma’aikatar Neja -Delta.

Shafin sashin Hausa na Muryar Amurka (BOA) ya ruwaito cewa Kotun Daukaka Kara ta yanke hukuncin sake zabe a tsakanin Akapabio na Jam’iyyar APC da wanda ya lashe zaben a PDP Sanata Christopher Ekpenyong a wasu mazabu.

Akpabio wanda ya fice daga PDP a lokacin yana Shugaban Marasa Rinjaye a Majalisar Dattawa, ya rubuta wa Shugaban Jam’iyyar APC, Mista Adams Oshiomhole cewa ba zai iya barin nauyin da Shugaba Buhari ya dora masa ya tafi maimaita zaben Sanata ba.

Lauya mai zaman kansa a Abuja Zubairu Namama ya ce matakin bai saba wa dokar zabe ba, don haka APC sai ta sake zaben fidda-gwani don samar da sabon dan takara.

APC ta bakin Sakataren Walwala Ibrahim Masari ta ce za ta ja hankalin Akpabio ya shiga takarar don ba wata dabara da ta wuce hakan.