✕ CLOSE Noma Da Kiwo Hotuna Kiwon Lafiya Girke-Girke Sana'o'i Kimiyya da Kere-Kere Ra'ayin Aminiya Ra’ayoyi Rahoto
Click Here To Listen To Trust Radio Live

‘Na gina masallaci da coci da kudin da na samu a satar yara’

Wani mai suna Taofeek Taiwo Lawal da ake zargi da satar kananan yara ’yan shekara 4 zuwa 7 yana karbar Naira dubu 100 kan yaro…

Wani mai suna Taofeek Taiwo Lawal da ake zargi da satar kananan yara ’yan shekara 4 zuwa 7 yana karbar Naira dubu 100 kan yaro daya daga hannun ubangidansa mai lakanin King da ke zaune a garin Osogbo a Jihar Osun, ya ce ya gina masallaci da coci da kudin da ya samu a satar.

Jami’an Kungiyar Yarbawa ta OPC ne suka kama mutumin a Ibadan bayan samun labarin sirri daga wata matar aure da aka sakaya sunanta. Kungiyar OPC shiyyar Olaifa a Ibadan a karkashin jagorancin Mista Babatunde Abiba ne ta a nuna  Taofeek Taiwo ga ’yan jarida inda ya furta da bakinsa cewa, “Ni dan asali kuma haifaffen garin Osogbo ne kuma ina cikin gungun mutum 15 da muke satar kananan yara a karkashin jagorancin ubangidanmu King. Na dade ina yin wannan aiki domin gaba dayan rayuwata ta dogara ce kan satar kananan yara.”

“Akwai lokacin da na sato dana na kawo aka biya ni Naira dubu 100 da na biya bukatata. Daga cikin irin wannan kudi da na tara ne na gina gidaje biyu da masallaci da coci a Osogbo tare da biyan kudin makarantar matata da ke karatu a wata babbar makaranta a garin Ile-Ife a Jihar Osun,” inji shi.

Ya ce “Na fi yin aiki a garuruwan Legas da Osogbo kuma sau biyar ana kama ni kan laifin satar yara inda ubangidana King yake yin belina bayan sasantawa da jami’an tsaro.  Iyayena suna sane da wannan aiki da nake yi,” inji shi.

Da yake amsa wata tambaya cewa, ya yi bai yi nadamar kamun da aka yi masa ba. “Sai dai a wani lokaci na yi kokarin tuba daga wannan aiki amma King ya ce, dole ne mu yi yarjejeniya a rubuce domin boye sirrinmu,” inji shi.

Kungiyar OPC ta mika mutumin ga Hukumar Tsaro ta Farin Kaya (NSCDC) wacce ta yi alkawarin yin binciken kwakwaf don gano maboyar abokan huldarsa da kama su tare da gurfanar da su a gaban kotu.