Search
Subscribe
Na gode matuka.  Allah Ya saka da alheri. Dakatar da hako ma’adinai a Jihar Zamfara

Na gode matuka.  Allah Ya saka da alheri. Dakatar da hako ma’adinai a Jihar Zamfara

A sakamakon yawan ayyukan ta’addancin da Jihar Zamfara take fama da shi yanzu Rundunar ’Yan sandan Najeriya ta sanar da dakatar da hako ma’adinai a jihar domin samun damar dakile ayyukan  ’yan ta’addan a fadin jihar.

Jihar Zamfara tana daya daga cikin jihohin da ke da dimbin ma’adinai a kasar nan wanda ya sanya akwai mutane da dama a ciki da wajen jihar da suke cin abinci ta hanyar hako ma’adinan da ke makare a karkashin kasar jihar.

Kamfanonin cikin gida da na kasashen ketare da dama suna amfana da dimbin ma’adinan da ke Jihar Zamfara, wadansu da amincewar hukuma suke hakowa, wadansu kuma ta haramtacciyar hanya, kuma irin wadannan su suka fi yawa.

Ko shakka babu ma’adinan sun taimaka wajen samar da aikin yi ga mutane da dama a ciki da wajen Jihar Zamfara tare da samar da masu arziki da dama, wanda hakan ya taimaka wajen rage batagari, domin masu zaman kashe wando ne suke zama matsala ga al’umma a mafi yawan lokuta.

Kwatsam sai aka wayi a farkon makon nan Shugaban ’Yan sanda Muhammad Abubakar Adamu ya bayar da sanarwa jim kadan bayan wani taro da suka yi a fadar Shugaban Kasa, cewa an dakatar da hako ma’adinai a Jihar Zamfara har sai abin da hali ya yi. Ya ce, an yi haka ne da nufin dakile ayyukan ’yan ta’adda a jihar, domin an gano cewa, masu hako ma’adinan suna da dangantaka da ’yan ta’addan.

Sai dai kuma a yayin da hukuma take ganin dakatar da hakar ma’adinai a Jihar Zamfara shi ne zai taimaka wajen dakile ’yan ta’adda, ya kamata kuma ta yi la’akari da cewa, yin haka zai iya sanya mutane da yawa su rasa aikin da suke yi, wanda hakan zai iya taimakawa wajen kara yawan masu zaman  kashe wando a jihar,  kuma matukar masu zaman kashe wando suka karu to babu shakka  masu aikata miyagun ayyuka za su karu, domin idan matsala ta yi wa mutune yawa takan sanya wani ya kasa daurewa har ya je ya aikata abin da bai dace ba.

Saboda haka maimakon dakatar da ayyukan hako ma’adinai a Jihar Zamfara kamata ya yi gwamnati ta himmatu wajen zakulo batagarin da ke cikinsu da nufin hukunta su, kuma za a iya samun karin bayani daga gare su game da yadda suke da alaka da ’yan ta’addan.

Haka kuma wajibi ne gwamnati ta himmatu wajen fito da hanyoyin rage radadin talauci a Jihar Zamfara, domin ’yan ta’addan sun taimaka wajen talauta dimbin mutane a jihar, sau da yawa wadansu ’yan ta’addan da aka kama cewa suke wahala ce ta sanya suka shiga wannan mugun aiki na garkuwa da mutane, domin an kashe duk ’yan uwansu kuma sun rasa komai nasu.

Lallai ne gwamnatin Jihar Zamfara ta mayar da hankali wajen yaki da talauci, duk abin da bai zama dole ba a bar shi, a rage barna da almubazzaranci da dukiyar jama’a, jami’an gwamnati su rage yawace-yawace, domin akwai shekarar da daukacin manyan Jihar Zamfara tun daga Gwamna da Mataimakinsa da shugabannin kananan hukumomi duk suka dunguma suka tafi Umara, alhali Allah bai wajabta musu yin haka ba, amma ya wajabta musu kula da talakawan jiharsu.

Mutanen jihar kuma ya kamata su gyara halayensu, su kiyayi aikita sabon Allah, su kasance masu rikon amana da kuma kamanta gaskiya tare da dukufa wajen yin addu’a dare da rana, domin addu’a ita ce takobin mumini.

Mun ga yadda addu’a ta yi tasiri lokacin da aka kama Alramma Ahmad Suleiman kwanakin baya, inda shi kansa Malam Ahmad ya ce a cikin kwana 13 da ya yi a hannun masu garkuwa da su ya sauke Alkur’ani sau biyar da rabi, sannan ga addu’o’in da mutane suke yi a wurare daban-daban. A sakamakon haka Malam Ahmad ya ce, masu garkuwa da su sun bayyana musu cewa sun shiga firgicin da ba su taba fuskantar irinsa ba. Malam Ahmad ya ce, yana ganin tasirin addu’o’in da suke yi ne da na sauran mutanen gari ya sanya ’yan ta’addan suka firgita, wanda har ya sanya aka samu baraka a tsakaninsu, har ta kai a karshe bayan an saki Malam Ahmad tare da mutanensa, aka kama wadansu daga cikin wadanda suka yi garkuwa da su din, wadanda suka bayyana cewa rikici ya barke a tsakaninsu bayan an saki Malam har sun kashe wadansu daga cikinsu. Wannan ya nuna cewa addu’a tana tasiri sosai a rayuwar jama’a.

Muna rokon Allah Ya kawo mana karshen fitintinun da suke damunmu, Ya kuma taimaka wajen samar da mafita. Masu aikata ayyukan ta’addanci kuma Allah Ya shiryar da su, Allah kuma Ya kare mu daga sharrinsu.

  • facebook
  • twitter
  • whatsapp
  • linkedin