✕ CLOSE Noma Da Kiwo Hotuna Kiwon Lafiya Girke-Girke Sana'o'i Kimiyya da Kere-Kere Ra'ayin Aminiya Ra’ayoyi Rahoto
Click Here To Listen To Trust Radio Live

…Na Gombe sun yi azamar maida rancen

Shugaban Kungiyar Manoman Shinkafa ta Kasa reshen Jihar Gombe kuma Shugaban Shirin Bayar da Rancen Noma (NECAS) a Jihar, Alhaji Ahmad Muhammad Dukku, ya ce…

Shugaban Kungiyar Manoman Shinkafa ta Kasa reshen Jihar Gombe kuma Shugaban Shirin Bayar da Rancen Noma (NECAS) a Jihar, Alhaji Ahmad Muhammad Dukku, ya ce a wannan karo manoman shinkafa a jihar sun yi kokari sosai wajen dawo da rancen da aka ba su.

Ya bayyana haka ne lokacin da yake zantawa da manema labarai kan kokarin da manoman shinkafar suka yi na dawo da bashin da aka ba su da amfanin gona; inda ya ce a karkashin kwamitin da suka kafa na dawo da rancen yanzu suna da akalla buhu sama da dubu uku na shinkafa a ajiye.

Ya ce dukkan wuraren ajiya na kungiyar a cike suke da buhunan shinkafar da manoman suka dawo da ita wanda rufen kan iyakoki da aka yi ya taimaka sosai wajen habaka noman musamman a Jihar Gombe.

Ya jinjina wa Shugaban Kasa Muhammadu Buhari kan yadda yake taimaka wa manoma musamman a shirin nan na Anchor Borrowers da ake bai wa manoma rance a bangarorin noma daban-daban na rani.

Ya ce a shirye suke su sake bai wa manoma wani bashin a shirin na noman rani saboda yadda suka biya bashin da aka ba su musamman manoman shinkafa.

Ya ce ce a kowace kadada daya idan manomi ya noma da kyau zai samu buhu 80 zuwa sama na shinkafa; amma abin da kungiyar take karba buhu 17 ne kawai daga manomin.

Ya yi kira ga ’yan Najeriya su yi addu’ar duk shugaban da zai gaji Buhari, ya zama mai kula da harkar noma sosai kamar yadda Buhari yake taimaka wa manoma a yanzu.

Cikin manoman shinkafar da Aminiya ta zanta da su Usman Ibrahim da Tukur Ya’u sun nuna gamsuwarsu da wannan shiri kuma sun yaba da yadda ake ba su wannan bashi na manoma inda suka yi addu’ar Allah Ya sa shirin ya dore.