✕ CLOSE Noma Da Kiwo Hotuna Kiwon Lafiya Girke-Girke Sana'o'i Kimiyya da Kere-Kere Ra'ayin Aminiya Ra’ayoyi Rahoto
Click Here To Listen To Trust Radio Live

‘Na harbi dana ne don na kare kaina’

Rundunar ’yan sandan Jihar Legas ta kame wani mutum mai suna Anthony Oyeniji, mai kimanin shekara 68 da ke zaune a unguwar Akowonjo kan zargin…

Rundunar ’yan sandan Jihar Legas ta kame wani mutum mai suna Anthony Oyeniji, mai kimanin shekara 68 da ke zaune a unguwar Akowonjo kan zargin harbin dansa da bindiga, wanda
ya dage kan ya yi haka ne ga dan nasa Taiwo don ya kare kansa daga yunkurin da dan ya yi masa da wuka.
Wata majiya ta bayyana cewa  Anthony da dansa Taiwo sun dade suna gaba da juna kan fadan da uban yake yi masa na rashin da’a da biyayya.
Majiyar ta ce a ranar da lamarin ya auku Taiwo ya dawo gida, sai mahaifin nasa ya rufe shi da fada kan ya gyara halayensa, sai kawai Taiwo ya shiga cikin dakin dafa abinci ya dauko wuka zai caka masa, sai shi kuwa ya dauko bindiga ya harbe shi a hannu.
Majiyar ta ci gaba da cewa sun bayyana cewa nan take sai hannun Taiwo ya karye daga bisani aka kai shi asibiti da ke kusa domin yi masa magani.
Mai magana da yawun ’yan sandan Jihar Legas, Ngozi Braide ta bayyana cewa suna ci gaba da bincike kuma da zarar sun kammala za su mika lamarin kotu. Sai kuma ta gargadi jama’a su guji  yin wasa da makami don yana iya jawo musu matsalar da ba su zata ba a rayuwa.