✕ CLOSE Noma Da Kiwo Hotuna Kiwon Lafiya Girke-Girke Sana'o'i Kimiyya da Kere-Kere Ra'ayin Aminiya Ra’ayoyi Rahoto
Click Here To Listen To Trust Radio Live

Na je Hajji sau goma a dalilin waka – Garba Gashuwa

Fitaccen mawakin Hausar nan da ya yi fice a wakokin siyasa da sauran wakoki Alhaji Garba Gashuwa, ba waka kadai ya tsaya ba har aikin…

Fitaccen mawakin Hausar nan da ya yi fice a wakokin siyasa da sauran wakoki Alhaji Garba Gashuwa, ba waka kadai ya tsaya ba har aikin gwamnati ya yi na tsawon wasu shekaru a Jihar Kano. Cikin zantawarsa da Aminiya a garin Gashuwa ya bayyana cewa ya mallaki komai na duniyar a dalilin waka:

Aminiya: Mene ne tarihinka a takaice?

Garba Gashuwa: Sunana Garba Gashuwa, ni ne dai mawakin nan ne da mutane suka sani ya yi suna a fagen waka da ta fito da sunansa ya shiga ko’ina sama da shekara 50 da suka gabata a dalilin waka, kuma na yi aiki da Gidan Talabijin na Kano na tsawon shekara 6 na kuma yi aiki da Hukumar Gidan Tarihi da Kula da Al’adu ta Kano nan ma na shekara 6.

Aminiya: Wadanne wakoki ka fi yi a cikin dangogin waka?

Garba Gashuwa: Ina wakokin siyasa da na gargadi da fadakarwa da wakar ilimi da tarbiyya har da yabon Annabi (SAW). Waka gaskiya babu irin wacce ba na yi.

Aminiya: Wace waka ce ta fi fice a cikin wakokinka da har ta fi daga sunanka?

Garba Gashuwa: Wakokina sun yi fice dukkansu sosai, amma babu kamar wacce na yi wa Tsohon Shugaban Kasa Ibrahim Badamasi Babangida, wanda nake jero baitoci nake cewa: “Wagga kasa mai kyau da abinci,

Duk inda ka noma za ka ga ka ci,

Ka ga mutum zai tashi a barci,

Ban da rashin kishi daga zuci,

Kai ta fi ni zan gyara kasata.”

Amshi: “Sannu da himma uban kasa Babangida mai son gyara kasata.”

Amma kafin Babangida ma ai na yi siyasa kuma na yi wakoki masu dama da suka yi tashe a lokacin.

Aminiya: Ganin ka jima kana waka yanzu wadansu na ganin tauraruwarka ta dushashe me ya kawo haka?

Garba Gashuwa: Idan tauraruwata ta dushashe ai lokaci ne. Ba ka gani rana ma tana faduwa idan ba ta faduwa ina ta jiya, ina kuma watan da ya kama jiya a wannan lokaci da muke hira da kai a yanzu. Komai lokaci ne.

Aminiya: Wace daukaka ka samu daga fara wakarka zuwa yanzu kuma wadanne nasarori ka samu?

Garba Gashuwa: Daukakar ita ce wacce da ka ji sunana ka neme ni, kuma sunana ya karade dukkan Najeriya da Afirka, ta inda a duk inda ka kira sunan Garba Gashuwa sai ka ji wani wanda ya ce eh ya san ni. Kuma duk abin da mutum yake nema a duniya na same shi dalilin waka domin Makka ma na je sau goma, na yi aure na hayayyafa ina da jikoki da gidaje ba gida ba, da motoci ba mota ba, kuma duk gwamnatin da aka yi a Jihar Kano sai na je Makka sau biyu da yake a Kano nake da zama.

Aminiya: Daga cikin ’ya’yanka akwai wanda ya gaje ka sana’ar waka?

Garba Gashuwa: Lallai akwai Musa Garba Gashuwa (MGG) wanda ya shahara a wajen yabon Annabi. Dana ne tare da shi muke waka shi ma ya iya na sallame shi.

Aminiya: Za mu iya cewa waka ta yi wa Garba Gashuwa sutura a rayuwarsa ke nan?

Garba Gashuwa: Kwarai da gaske domin waka ta sa sunana ya shiga duniya na samu daukakar da nake da ita har ya sa mutane idan suka ji sunana suke rububin son ganina a koyaushe.

Aminiya: Ganin shekaru sun cim maka ko kana da niyyar barin waka tunda kana da magada?

Garba Gashuwa: Ina shekarun suke? Na kai Shata ne da ya kai shekara 80 yana waka?  Ni kuma shekara 50 na yi fa ina waka, ka ga ashe da saurana kuma ita waka ba maganar shekaru a cikinta.

Aminiya: Wane kira kake da shi zuwa ga ’yan uwanka mawaka?

Garba Gashuwa: Kirana shi ne su mayar da hankali wajen yin abin da yake gabansu bil hakki da gaskiya don ko kwasar kashi kake yi, idan ka rike shi da gaskiya za a ce wane ya fi iya kwashe masai mai kyau a nemo shi haka wakar ma. A bar yin zambo da cin  mutunci.

Aminiya: Ganin ka shahara a harkar waka me kake son a  rika tuna ka da shi ko bayan ba ranka?

Garba Gashuwa: Ko bayan ba raina a rika yi min addu’a da zarar wani ya ambaci sunana saboda mun bada gudunmawa a harkar waka wajen kawo gyara a bangarori daban-daban a duniya ba ma a kasar nan kadai ba.