✕ CLOSE Noma Da Kiwo Hotuna Kiwon Lafiya Girke-Girke Sana'o'i Kimiyya da Kere-Kere Ra'ayin Aminiya Ra’ayoyi Rahoto
Click Here To Listen To Trust Radio Live

Na ji dadin dawo da buga jaridun Daily Trust a Maiduguri – Gwamna Zulum

Gwamna Jihar Borno Farfesa Babagana Umara Zulum ya bayyana farin cikinsa kan yadda Kamfanin Media Trust ya dawo da buga jaridun Daily Trust da Aminiya…

Gwamna Jihar Borno Farfesa Babagana Umara Zulum ya bayyana farin cikinsa kan yadda Kamfanin Media Trust ya dawo da buga jaridun Daily Trust da Aminiya a Maiduguri.

Gwamnan ya bayyana haka ne a shekaranjiya Laraba lokacin da ya kai ziyara harabar kamfanin, inda Babban Jami’in Zartarwar Kamfanin Malam Mannir Dan Ali ya zaga da shi.

Kafin ziyarar sai da manyan jami’an kamfanin suka gana da Gwamna Zulum a Gidan Gwamnati.

Gwamna Babagana Zulum ya ce hakika yana farin ciki, kuma yana alfahari ganin kamfanin ya dawo da buga jarida a Borno, inda ya ce yin hakan zai taimaka wajen samar da ayyukan yi ga jama’a, musamman jama’ar Jihar Borno.

Ya ce, zai ba kamfanin duk goyon bayan da yake bukata, inda ya ce shekaru da dama yana bibiyar jaridun Daily Trust kuma ya ce shekaru da dama yana ganin yadda ake kawo jaridar daga Kano a kullum, domin ganin jaridar ta iso Maiduguri cikin lokaci don amfanin al’umma.

Gwamna Zulum ya ce kamfanin ya dauki duk wani mataki, don ci gaban Jihar Borno, “Ina fadar hakan ne, domin ganin koda rana daya ba a daina kawo jaridar nan Maiduguri ba,” inji shi.

A jawabin Malam Mannir Dan Ali ya gode wa Gwamna Zulum domin kawo wannan ziyarar, sannan ya bada tabbacin kamfanin zai ci gaba da yin ayyukansa na bayar da labarai yadda ya kamata.