✕ CLOSE Noma Da Kiwo Hotuna Kiwon Lafiya Girke-Girke Sana'o'i Kimiyya da Kere-Kere Ra'ayin Aminiya Ra’ayoyi Rahoto
Click Here To Listen To Trust Radio Live

‘Na kashe rayuka sama da 200 a hare-haren Boko Haram’

Wani jigo a kungiyar Boko Haram, mai suna Umar Abdulmalik da jami’an ’yan sanda na musamman (IRT) a karkashin Mataimakin Kwamishinan ’Yan Abba Kyari suka…

Wani jigo a kungiyar Boko Haram, mai suna Umar Abdulmalik da jami’an ’yan sanda na musamman (IRT) a karkashin Mataimakin Kwamishinan ’Yan Abba Kyari suka kama a makon jiya ya bayyana dalla-dalla yadda kungiyar ta shirya tayar da bam din da ya tashi a Nyanya a shekarar 2014 da kuma harin da aka kai a gidan yarin Jihar Kogi inda ake tsare da wadansu ’ya’yan kungiyar.

A ranar Alhamis din makon jiya ce ’yan sanda suka kama Abdulmalik a gidan ’yar uwarsa da ke Unguwar Igando a Jihar Legas inda ya tafi jinyar raunin da aka yi masa da harsashi.

A yayin da yake amsa tambayoyin da ’yan sanda, Abdulmalik ya ce bama-baman da aka yi amfani da su a harin Nyanya da hannu aka kera su a Jihar Kogi. Ya kuma shaida wa ’yan sanda yadda ya jagoranci wadansu ’ya’yan kungiyar suka kai hare-hare a bankuna da kuma yin fashi da makami da kashe-kashen mutane a Abuja da Owo a Jihar Ondo da kuma Lakwaja a Jihar Kogi.

Abdulmalik ya shaida wa ’yan sandan cewa ya kashe akalla mutum 200 kafin a kama shi. Ya ce wani mai suna Malam Mustapha da suka hadu a shekarar 2009 ne ya shigar da shi kungiyar Boko Haram. “Na shiga kungiyar Boko Haram ce a Okene a karkashin jagorancin wani mai suna Zaidi kuma mun tayar da bama-bamai a Kaduna da Kano da Abuja. Zaidi ne ke samar da bama-baman, ni kuma aikina shi ne kai bama-baman wuraren da muke niyyar kai hari. Bayan wani lokaci, DSS sun gano kungiyarmu inda suka fara kama mambobinmu ciki har da Malam Mustapha kuma daga baya aka rushe masallacinsa,” inji shi.

Ya kara da cewa, “Mun yanke shawarar fara yin fashi a bankuna ne lokacin da kudadenmu suka kare. Zeedi ya kawo mana bindigogi kuma ya ce mu kai hari gidan yarin Okene domin mu ceto ’yan uwanmu. Mun yi nasara a harin da muka kai kuma daga bisani muka yi fashi a wasu bankuna a Okene. Daga baya mun koma garin Owo inda muka sake yi wa wasu bankuna fashi inda muka samu karin kudi na sayen makamai da hada bama-bamai amma daga baya an kama Zaidi da wasu mambobinmu.”

Ya ce, “Haka ya sa muka tafi Abuja da bama-baman da muka kera muka kafa sabuwar kungiya a shekarar 2014 kuma muka kai hare-hare ciki har da na Baned Plaza da Nyanya da Kuje da wasu wurare amma daga baya asirinmu ya tonu kuma aka kwace sauran bama-bamanmu. Na yi sa’a ba a kama ni ba, sai na tsere zuwa Kano na buya na tsawon shekara biyu daga baya na dawo Abuja na hada sabuwar kungiyar fashi da makami.”

Ana zargin kungiyarsa ce ta rika kashe ’yan sanda tana gudu da bindigoginsu, kuma bayan da aka gano su ne aka kai musu farmaki inda aka raunata shi amma ya tsere zuwa Legas, kafin a bi shi a kamo shi