✕ CLOSE Noma Da Kiwo Hotuna Kiwon Lafiya Girke-Girke Sana'o'i Kimiyya da Kere-Kere Ra'ayin Aminiya Ra’ayoyi Rahoto
Click Here To Listen To Trust Radio Live

Na mallaki gida da mota a wasan dambe – Shamsu kanin Emi

Aminiya ta samu tattaunawa da matashin dan damben gargajiya Shamsu Kanin Emi wanda aka fi sani da ‘Dan-zaki’ kafin a kammala wasan karshe a filin…

Aminiya ta samu tattaunawa da matashin dan damben gargajiya Shamsu Kanin Emi wanda aka fi sani da ‘Dan-zaki’ kafin a kammala wasan karshe a filin dambe na Deidei da ke Abuja gab da shigowar Ramadan har sai bayan salla.  Ga yadda hirar ta gudana:

Mene ne cikakken sunanka?

Sunana Shamsu kanin Emi amma an fi sanina da Dan zaki.

 Shekara nawa ka shafe a sana’ar dambe?

Na shafe kimanin shekara 9 zuwa 10 a wasan dambe kuma na samu rufin asiri a ciki domin na yi gida, na yi mota kuma ina taimakawa ’yan uwa da abokan arziki. Babu abin da zan ce da wasan dambe sai godiya ga Allah, kuma a yanzu haka akwai yara da suke tare da mu suna koyon harkar wasan dambe kuma in dai sun ci gaba da yin biyayya to za su dace su ma su kai ga babban matsayi nan gaba.

Kana alfahari da wasan dambe?

Gaskiya wasan dambe wasa ne da nake alfahari da shi kwarai da gaske domin a halin yanzu shi ne sana’ata kuma ya rufa mini asiri domin na rike shi sana’a kuma da gaske nake yi shi ya sa nake samun nasara a kan wasu daga cikin manya kuma shahararrun ’yan dambe.

Wadanne shahararrun ’yan dambe ka taba karawa da su?

Akwai Ebola. na kara da shi kuma na samu galaba a kansa, sannan mun fafata da Dan-auta wanda shi ma babba ne kuma fitacce a wasan dambe ga Babangida Kende da Dogon-Auta Allah ya jikansa. Sannan na fafata da Mai takwasara wanda shi kuma sau biyu yana kashe ni a wasa daban-daban amma ina nan ina shiri wata rana sai na kashe shi. Don haka ni ina alfahari da wasan dambe kuma na rike shi sana’a.

Shin a ra’ayinka ya dace a rika tallafawa wasan damben gargajiya don ya bunkasa a kasar nan?

Ya  kamata masu kudi wadanda suke sha’awar harkar dambe su zuba jari don bunkasa wasan dambe musamman a bangaren gina filayen wasanni da daukar nauyin ’yan wasa, domin harka ce da za ta kawo riba  kuma za ta rage zaman kashe wando tsakanin matasa kuma ta bunkasa kudin shiga ga hukuma. Don haka ina kira ga masu kudi su sanya jari a cikin harkar dambe domin za su ci riba kuma za su taimakawa matasa.

Ita kuma Gwamnati ya kamata ta sanya damben gargajiya a cikin jerin wasannin kasar nan, yin hakan zai bunkasa yawon bude ido musamman a ce ana yin damben duk shekara ana shirya wata babbar gasa wacce hukuma za ta rika kulawa da ita. musamman gwamnatocin Arewa tun da mafi yawa ’yan Arewa sun fi yi kuma yana tana sa nishadi. Su kuma matasa su rungumi harkar dambe domin tana da rufin asirin kuma tana hana zaman kashe wando.

Wane kira gare ka ga matasan ’yan dambe?

’Yan uwana matasa ’yan dambe lallai ya kamata mu dage mu riki wannan harkar a matsayin sana’a domin ta haka ne za mu samu nasara a kan  harkar, sannan mu yi biyayya ga na gaba domin sai da biyayya ake kaiwa ga nasara kuma mu dage da yin addu’a. Sannan mu tsaftace kanmu daga shaye-shayen miyagun kwayoyi domin shaye-shaye yana lalata rayuwa kuma shi ya sa wasu suke kyamar mu suna ganin filin wasan dambe tamkar waje ne na marasa tarbiyya. Shi ya sa wasu matasan suna da sha’awar harkar amma saboda wasu gurbatattu a harkar sun kasa shiga ciki.   Lallai mu dauki wannnan wasa kamar mutum ne da zai tafi gonarsa ko kasuwa idan muka yi haka lallai za mu ga ci gaba.  A ganina, wasan dambe ya fi aikin gwamnati rufin asiri.

Wane Kira kake da shi ga gwamnati?

Ina amfani da wannan dama don yin kira ga gwmanatin tarayya da ta gina mana filayen wasanin dambe a cikin fadin kasar nan sannan ta rika sanya wata gasa a tsakanin matasa domin yin haka zai kara habaka wasan dambe sannan zai jawo masu yawon bude ido su rika shigowa kasar nan.   Haka ma gwamnonin jihohi su rika sanya gasa a tsakanin matasa, sannan a shigo ciki a tsaftace  harkar domin ta dace da zamani.  Kodayake wasu sun ce za su dauke mu zuwa kasashen waje bayan sallah domin yin harkar to amma dai ya kamata gwamnati ta shigo da mu cikin tsarinta na farfardo da rayuwar matasa. Su ma Sarakuna ya kamata su shigo cikin harkar domin ta su ce tun da abun ya shafi gargajiya.

A hagu, Shamsu Qanin Emi daga Arewa da Babangida Kende daga Guramaxa kafin su gwabza
A hagu, Shamsu Qanin Emi daga Arewa da Babangida Kende daga Guramada kafin su gwabza