Da Dumi Dumi

Na sayar da itace da kosai kafin in zama farfesa – Andrew Haruna

Andrew Haruna

Farfesa Andrew Haruna ya fito ne daga garin Gar a Karamar Hukumar Alkaleri a Jihar Bauchi, yanzu shi ne Shugaban Jami’ar Tarayya da ke Gashuwa (FUGA) a Jihar Yobe. Farfesan wanda shi ne  Shettiman Ilimin Masarautar Tikau a Karamar Hukumar Nangere a Jihar Yobe, shi ne Wakilin Raya Kasar Tangale a Masarautar Billiri a Jihar Gombe. A zantawarsa da Aminiya ya bayyana gwagwarmayar da ya sha a rayuwa da burin da yake da shi kan samar da ilimi a jam’iar da yake shugabanci:

Mene ne takaitaccen tarihinka?

An haife ni a 1957 a garin Gar da ke Karamar Hukumar Alkaleri a Jihar Bauchi. Na tashi a kauyenmu ina matukar son yin karatu, ina son zuwa makaranta amma iyayena ba su da kudin da za su biya mini. Dole sai na fara yin noma da tallar kosai da sayar da itace kafin in samu kudin da nake biya wa kaina makaranta. Na karatu a makarantar firamaren Gar daga 1964-1970. Na shiga Kwalejin Gwamnati da ke Maiduguri daga 1971 -1975.

A wancan lokacin idan za mu koma makaranta mutum zai shiga manyan motocin dakon kaya ne tun daga Gar zuwa Maiduguri tafiya mai nisan kilomita 600, don haka idan zan koma makaranta sai  in rugume ’yan kayana cikin mota in yi tafiyar kwana da kwanaki zuwa Maiduguri. Idan ba ni da kudi nakan roKi direba ya taimaka ya dauke ni kyauta.

Yaya ka karasa makarantar?

ADVERTISEMENT

Lokacin da muka yi jarrabawar kammala makarantar sai Allah Ya ba ni sa’a na samu sakamako mai kyau. Don haka sai na yi shawarar in tsaya a Maiduguri maimakon in koma kauyenmu. Kuma dalilin da ya sa na tsaya shi ne don ina so in ci gaba da karatu a jam’ia amma kamar yadda ka sani ba ni da kudi. An ce babu maraya sai rago, shi ke nan sai na zama samu wuri a wajen Gidan Waya (Post Office) a gindin wata bishiya ina gyaran takalma ina wankewa, a nan nake samun ’yan kudi. Kuma zan iya tunawa ana yawan ganin fuskata a gidan rediyo da talabijin na Maiduguri don nakan je in share musu ofishin, kuma ma’aikatan sukan aike ni daga wannan wuri zuwa wancan.

Yaya ka yi ka ci gaba da karatu?

Ina iya tunawa wata rana da wata mace ta nemi in yi mata aiki, sanadiyyar wannan mata da Allah Ya turo min rayuwata ta sauya. Ta zo ne ina gyara mata takalma muna zance, sai mamaki ya rufe ta da na ce mata na yi makarantar sakandare. Sai ta tausaya mini kuma da taimakonta Allah Ya sa na samu shiga makarantar share fagen shiga Jami’ar Maiduguri daga 1976 -1978, kuma daga nan sai na samu aka dauke ni a jami’ar in karanta Ilimin Harsuna kuma a 1981 na samu digiri mai cike da yabo. Na yi hidimar kasa a Kwalejin Gwamnati da ke Sakkwato inda na karantar a Kwalejin Kimiyya da Sana’a da ke Sakkwato. A 1982 sai aka dauke ni aiki a matsayin malami a Jami’ar Maiduguri kuma a tsakanin 1983 zuwa 1990 lokacin ne, Jam’iar Maiduguri ta tura ni kasar Ingila don in karo ilimi na samu shiga wata jam’ia.

Wadanne ayyuka farfesa ya yi a jami’a?

Gaskiya suna da yawa, a 1982 aka dauke ni malami a jam’ia, kuma a  shekarar 2006 na zama cikakken farfesa, saboda aiki tukuru da na yi, wanda wannan shi ne ya sa na kasance mutum na farko da ya zama Farfesa a kauyenmu Gar da ke Jihar Bauchi.

Ta yaya ka zama farfesa?

Kasan lokacin da Jami’ar Maiduguri ta tura ni karatu a Ingila daga 1983-1990 a can ne na yi digiri na biyu da na uku. Kuma a tsakanin shekarun 1985 zuwa 1990 har ma na samu kyautar kudi saboda na kasance ni ne dalibin da ya fi fice wajen samun nasarar digiri na uku a fannin da na karanta na furta kalami (Phonethics) a Jam’iar Ingila. Na samu lambobin yabo a ciki da wajen Najeriya don yin ayyuka masu kyau da kuma taimakon al’umma. Na kuma wallafa littattafai sama da 40. Haka dai na yi ta gwagwarmayar koyarwa da koyon karatu a jami’oin kasashen Ingila da Jamus da Switzerland da Austireliya.

Yaushe ka zama Shugaban Jami’ar Tarayya ta Gashuwa?

An nada ni a shekarar 2016, kuma ina matukar godiya ga Shugaban Kasa Muhammadu Buhari saboda wannan dama da ya ban i don in taimaka wa kasata. Ka san kafin wannan mukami na yi ayyuka a kasa da kuma Jihar Bauchi don a shekarar 2011-2015, na kasance Shugaban Majalisar Gudanarwa ta Kwalejin Kimiyya da Sana’a ta Abubakar Tatari Ali da ke, Bauchi. Sannan a 2014 na zama wakili taron fasalta makomar kasa a 2014, kuma na yi aiki a manyan kwamitocio masu muhimmanci a taron. A shekarar 2015 na kasance Shugaban Kwamitin Kwalejin Kimiyya da Sana’a da ke Auchi. Ni waliki ne a Kungiyar Kare Muradun Arewa (ACF), kuma na taba kasancewa Sakataren Samar da Zama Lafiya a karkashin jagorancin Alhaji Lema Jibril (Dan Iyan Katsina). Sannan a tsakanin shekarar  2015-2018, na kasance wakili a Hukumar Amintattun Jami’ar Bingham da ke Karu a Jihar Nasarawa, kuma yanzu ni ne Shugaban Kungiyar Shugabannin Jami’o’in da aka kafa karo na uku a Najeriya, wadanda suke kiran kansu manyan jami’o’in kasar nan guda 12 .

Yaya kake fama da wannan mukami?

A gaskiya na dauki wannan nadi da aka yi mini a matsayin Shugaban Jami’a a matsayin kalubale, kuma na dauke shi cewa an ba ni dama ne domin in ba da gudunmawata wajen ciyar da ilimi gaba a kasar nan musamman a wannan shiyya tamu ta Arewa maso Gabas. Kuma na maida hankali ne don in samar da yanayin da matasa ’yan Najeriya da dama za su samu ilimin jami’a cikin sauki da nufin samar da ilimi mai nagarta.

Me kake so a tuna da kai bayan ka bar shugabancin Jami’ar FUGA da ke Gashuwa?

Burina shi ne in samar da hanyar da Jami’ar Tarayya ta Gashuwa za ta kasance jami’a tagari da ta fi inganci cikin jami’o’in kasar nan. Don ina ganin duk da karancin kudin gudanar da jami’ar da ta ake fama da shi idan aka yi tattali, za a iya samar da sauyin da zai kawo ci gaban da ake fata a jami’ar. Domin a gaskiya ina gani a nan garin Gashuwa ina ji kamar ina gida ne Gar. A kullum rayuwar Gashuwa na tuna mini yadda na tashi a kauyenmu, daga dan talaka na zama babban malamin jami’a, ina tuna irin taimakon da Allah Ya yi mini a kullum kuma ina tunanin yaya zan yi ni ma in taimaki dalibaina wadanda ke gwagwarmayar zama wani abu a rayuwa ta hanyar karatunsu. Kuma har abada zan ci gaba da godiya ga ’yan uwana ’yan Najeriya wadanda da kudin harajinsu ne aka yi amfani da su na samu ilimi, kuma ina kara godiya ga Gwamnatin Najeriya da ta ba ni dama na je makaranta na yi karatu. Ni a gaskiya ina ganin Najeiya ta yi mini komai ni ma kuma yanzu lokaci ne da ya kamata in biya kasata ta hanyar yi wa al’ummar kasata aiki tukuru a duk inda na samu kaina in dai ina raye.

Share
A latsa wannan alamar domin shiga zauren Jaridar Aminiya