✕ CLOSE Noma Da Kiwo Hotuna Kiwon Lafiya Girke-Girke Sana'o'i Kimiyya da Kere-Kere Ra'ayin Aminiya Ra’ayoyi Rahoto
Click Here To Listen To Trust Radio Live

‘Na sayi shanu 10 da kudin fansa da na karba’

Wani matashi  mai kimanin shekara 24 da ake zargi da garkuwa da mutane, mai suna Bello Abdullahi ya ce ya sayi shanu goma a kauyensu…

Wani matashi  mai kimanin shekara 24 da ake zargi da garkuwa da mutane, mai suna Bello Abdullahi ya ce ya sayi shanu goma a kauyensu da ke Jihar Yobe a kan Naira dubu 450 da ya samu bayan sun sace wani dan kasuwa Alhaji Abubakar Bashar.

Bello Abdullahi ya ce su shida ne suka yi wannan aika-aika inda shugabansu ya bayyana musu cewa sun amshi Naira miliyan  20 kafin suka sako Alhaji Bashar.

Ya ce sun yanke shawarar  sace   Alhaji Abubakar Bashar ne a wajen wani yaro mai kiwon shanu inda ya bayyana musu ko wane ne Abubakar din.

Bello ya amsa laifinsa na sace Bashar bayan ’yan sanda sun kama su a ranar Litinin da ta gabata. “Mu shida ne muka yi garkuwa da Bashar sannan shugabanmu ya fada mana cewa an ba mu Naira miliyan 20 ne sannan aka ba ni nawa kason inda na sayi shanu goma a kauyenmu a Yobe. Kuma Mun samu labarin Bashar ne a wajen wani yaro mai kiwon shanu,” inji shi.

Kakakin Rundunar ’Yan sandan Jihar Adamawa, DSP Suleiman Nguroje ya ce Abdullahi da sauran abokan zarginsa dubunsu ta cika  ne saboda suna addabar jihar da aikata miyagun halayen Allah wadai.

Ya ce sashin bincikensu ne ya zurfafa bincike kan matasan, inda suka yi nasarar kama mutum biyu, sauran hudun ma ana ci gaba da nemansu har sai an kama su a hukunta su kamar yadda doka ta tsara.