✕ CLOSE Noma Da Kiwo Hotuna Kiwon Lafiya Girke-Girke Sana'o'i Kimiyya da Kere-Kere Ra'ayin Aminiya Ra’ayoyi Rahoto
Click Here To Listen To Trust Radio Live

Na sha dukan Taiwo Awoniyi don hana shi buga kwallo a lokacin da yake karami -Mahaifinsa

Mista Solomon Awoniyi, a karshen makon jiya ne ya bayyana yadda ya kusa ya hana dansa Taiwo Awoniyi buga kwallo a lokacin da yake karami,…

Mista Solomon Awoniyi, a karshen makon jiya ne ya bayyana yadda ya kusa ya hana dansa Taiwo Awoniyi buga kwallo a lokacin da yake karami, hasalima mahaifin ya ce ya sha zane Awoniyi da bulala a mafi yawan lokuta don hana shi zuwa filin kwallo.

Mista Solomon Awoniyi ya bayyana haka ne a gidansa da ke Ilori a lokacin da yake hira da manema labarai jim kadan bayan shugaban kasa Goodluck Jonathan ya yi wa daukacin ’yan kwallon Golden Eaglets da jami’ansu ruwan Naira a ranar Lahadin da ta wuce bayan sun samu nasarar lashe kofin duniya na matasa da ya gudana a Hadaddiyar daular Larabawa a karo na hudu a makon jiya.
Mahaifin ya ce, tun Taiwo Awoniyi yana karatu a matakin firamare yake da sha’awar buga kwallo. Ya ce sau da dama iyalansa kan bazama nemansa idan suka ga bai dawo daga makaranta ba, amma da zarar sun halarci filin kwallo sai su tarar da dansu ya yi gumi sharkaf ana buga kwallo tare da shi.
“Nakan zane shi da bulala don ganin ya daina zuwa filin kwallo amma kamar ma ina zuga shi ne, daga baya ne na hakura na zura ido na ga yadda rayuwarsa za ta kasance bayan na yi masa addu’ar fatan alheri. Yau ga shi dana ya janyo mana arzikin da ba mu taba tsammani ba ta hanyar buga kwallo bayan sun lashe kofin duniya na matasa. A gaskiya ba zan manta da wannan rana ta farin ciki ba”, inji Mista Solomon Awoniyi.
Daga nan sai mahaifin ya jinjinawa kocin Awoniyi Rasak Olojo da ya koyar da shi harkar kwallo.
Ya ce kafin wannan lokaci dansa yana daya daga cikin ’yan kwallon da suka fafata a gasar cin kofin Koka-Kola da aka yi a garin Ibadan da hakan ta sa aka dauke su zuwa Landan a shekarar 2010 bayan sun samu nasara. Ya ce masu horarwa Nduka Ogbade da Seyi Olofinjana da suka kasance mataimakan kocin Golden Eaglets Manu Garba ne suka zakulo Taiwo kuma suka sanya shi a cikin kungiyar kwallon kafa ta Golden Eaglets da suka tafi Dubai aka fafata da su.
Ya ce ko a shekarar 2010 Taiwo Awoniyi an zabe shi dan kwallon da ya fi nuna kwazo (Most baluable Player) a birnin Ladan a gasar da suka buga a shekarar 2010.
Shi dai Mista Solomon Awoniyi, tsohon dan sanda ne kuma yanzu haka yana zaune tare da iyalinsa a Ilorin yana cigaba da gudanar da rayuwarsa.