Da Dumi Dumi
ADVERTISEMENT

Na shiga kungiyar asiri dan na yaki makiyana – Dan shekara 14 

Wani yaro dan makarantar karamar sakandare dan shakara 14 mai suna Christoper Anthony, ya bayyana cewa ya shiga kungiyar asiri ne domin ya yaki makiyansa ya kuma kece raini a tsakanin ‘yan uwansa dalibai.

Majiyar mu ta shaida cewa, yaron dan unguwar Mutum Guda da ke Karamar Hukumar Karu a jihar Nasarawa, ya amsa laifinsa na shiga kungiyar asiri a lokacin da rundunar ‘yan sandan jihar  ta gabatar da shi ga ‘yan jaridu

ADVERTISEMENT

Majiyar ta ce, ko a kwanakin baya ma Hukumar ‘yan sandan ta gabatar wa manema labarai ‘yan kungiyar asiri 34 wadanda akasarin su ‘yan makarantun sakandare ne a Karamar Hukumar ta Karu. Kwamishinan ‘yan sandan jihar Bola Longe, ya yi kira ga iyaye da su dinga sanya idanu akan ‘ya’yan tare da basu tarbiya ta gari, ya ce Hukumar baza ta yi kasa a gwiwa ba wajen kawar da kungiyoyin asiri a jihar.

A jihar Legas ma Hukumar ‘yan sandan ta tashi haikan wajen yaki da ‘yan kungiyar inda a bayabayan nan takame mutum 100 a mako guda wadanda ake zargi da shiga kungiyar asiri.

ADVERTISEMENT