✕ CLOSE Noma Da Kiwo Hotuna Kiwon Lafiya Girke-Girke Sana'o'i Kimiyya da Kere-Kere Ra'ayin Aminiya Ra’ayoyi Rahoto
Click Here To Listen To Trust Radio Live

Na yaye mutum 52 a sana’ar faci – Faruku Maifaci

Malam Faruku Maifaci da ke zaune a kusa da Ma’aikatar Ayyuka ta Jihar Kebbi kuma ya shafe shekara 35 yana sana’ar faci a Birnin Kebbi,…

Malam Faruku Maifaci da ke zaune a kusa da Ma’aikatar Ayyuka ta Jihar Kebbi kuma ya shafe shekara 35 yana sana’ar faci a Birnin Kebbi, shi ne Shugaban Kungiyar Masu Faci ta Jihar Kebbi, ya shaida wa Aminiya cewa ya yaye yara 52 a wannan sana’a ta faci:

 

Aminiya: Mene ne takaitaccen tarihinka?

Faruku Maifaci: Ni mutumin cikin garin Birnin Kebbi ne. Na yi makarantar firamare da sakandare a nan Jihar Kebbi. Kuma na fara koyon wannan sana’a ta faci  ce tun ina karami. Yau kimanin shekara 32, a wannan sana’a ta faci na yaye yara 52. Yanzu haka, duk sun zama masu cin gashin kansu. Daga cikinsu ma akwai wadanda suka yaye wanda suka koya musu. Ka ga sun zama jikokina ke nan a sana’ar faci. A halin yanzu ina da yara 27 da ke koyon aiki a wurina, kuma nan ba da dadewa ba daga cikinsu zan yaye yara 12.

 

Aminiya: Wadanne nasarori ka samu da wannan sana’a?  Faruku Maifaci: Ina farin ciki da wannan sana’a tawa saboda da ita na mallaki gida, sannan na aurar da ’ya’yana. A cikinta nake daukar hidimar dukkan iyalina kuma cikinta nake taimaka wa ’yan uwana kuma na mallaki filaye da dabbobi duk da sana’ar faci. Daga cikin yaran da na koya wa aiki akwai ’ya’yana na cikina wadanda yake yanzu su ma sun zama kwararru a sana’ar faci.

 

Aminiya: Wadanne matsaloli kake samu a wannan sana’a?

Faruku Maifaci: Na samu matsaloli iri-iri da fara wannan sana’ar tawa ta faci. Kamar rashin samun aiki daga wurin mutane da rashin wadatar kayan aiki. Saboda lokacin da na fara wannan sana’a nakan fito da wuri, amma ban samu ko kwandala ba. Haka na yi ta hakuri da juriya. Akwai wata babbar matsala da duk mai sana’ar faci yake fuskanta, idan ana ba taya iska wata takan fashe ta ji wa masu wannan sana’a rauni. Kamar a kwanan nan daya daga cikin yarana ya samu irin wannan matsala, inda babbar taya ta fashe ta karya yarona  har wuri uku, sai da muka kai shi asibitin kashi na Dala da ke Kano.

 

Aminiya: Za ka iya kiyasta abin da kake samu daga wannan sana’a kullum?

Faruku Maifaci: A kowace rana idan na fito, idan Allah Ya sa akwai alheri, nakan samu Naira dubu takwas zuwa dubu 10, wata rana kuma haka zan fito in koma gida ba tare da na samu komai ba.

 

Aminiya: Ko kana da sha’awar  barin wannan sana’a idan ka samu jari?

Faruku Maifaci: A gaskiya ko na samu jari ba zan iya barin wannan sana’ar tawa ba, saboda tsawon shekarun da na samu a cikinta kuma na samu alheri. A yanzu idan na samu jari abin da zan yi shi ne kawai zan karo kayan aiki na zamani kuma in sayi tuwaris na tayoyin mota da babur domin ni ma in rika sayarwa. Duk da yake Hukumar Kiyaye Hadurra ta Kasa tana gargadin jama’a kan amfani da tayoyin tuwaris. Najeriya dole a yi amfani da tayoyin saboda yanzu ba mu da kamfanonin yin sababbin tayoyi kamar yadda muke da su a da a Kaduna. Kodayake, na ji an ce Shugaba Buhari zai farfado da Kamfanin.

 

Aminiya: Mene ne gaskiyar zargin da mutane ke yi cewa wadansu masu sana’a irin taku suna saka allura cikin ruwan faci, idan mutum ya kawo aiki sai su huda masa tib, domin su yi masa karin kudi?

Faruku Maifaci: Eh, to  idan hakan na faruwa ma, ba na daya daga cikinsu. Kuma duk mutumin da ya sa cuta a rayuwa ko harkar sana’arsa, to zahirin gaskiya ba zai taba ganin ci gaba ba. Amma ita gaskiya, a ko’ina take bayyana kanta.

 

Aminiya: Wane kira za ka yi ga matasa kan su daina raina kananan sana’o’i irin naku?

Faruku Maifaci: Kiran da zan yi ga matasa shi ne, wannan harkar faci da suke gani sana’a ce mai matukar ban sha’awa. Idan har matashi ba zai sa girman kai a rayuwarsa ba, idan ya rike ta, sana’a ce da za ta iya rike mutum da iyalinsa tsawon rayuwarsa. Kuma ina kara kira ga masu sanao’in hannu da su rika taimakawa suna daukar matasa suna koya musu irin sana’o’in da suke yi, domin kauce wa zaman banza ga matasa. Kuma iyaye su ba da hadin kai wajen tura ’ya’yansu koyon sana’o’in hannu domin dogaro da kai

 

Aminiya: Ga gwamnati fa?

Faruku Maifaci: Kirana ga gwamnati shi ne ta rika tallafa wa masu sana’ar hannu. Wato irin sana’o’inmu, musamman ganin wadannan sana’o’i za su rage matsalolin rashin aikin yi ga matasammu. Kuma ina kira ga gwamnatin Jihar Kebbi ta tallafa wa masu sana’ar faci da kayan aiki irin na zamani, domin yanzu a duniya an samu ci gaba a fannin kowace irin sana’a.