Search
Subscribe
Na yi asarar Naira tiriliyan 2 bayan hawana mulki – Trump

Shugaban Amurka Donald Trump

Na yi asarar Naira tiriliyan 2 bayan hawana mulki – Trump

Shugaban Amurka Mista Donald Trump ya ce ya yi asarar Dala biliyan 2 zuwa 5 (kimanin Naira tiriliyan 2) bayan hawansa kujerar shugabanci Amurka, saboda harkokin kasuwancinsa sun ja baya. Ya ce hakika harkokin kasuwancinsa sun ja baya tun shigarsa siyasa, wanda hakan babu abin da ya jawo masa in ban da hasara.

Sai dai wannan hasashe na Donald Trump babu wata kwakwarar shaidar da za ta tabbatar da haka, domin Trump bai bayyana adadain kadarorinsa ba, kamar yadda sauran shugabannin Amurka suke yi.

A wani rahoto da mujallar Times ta fitar a watan Maris ta ce babu sahihin zance da ke nuni da cewa ya yi asarar Naira tiriliyan 2 tun zamowarsa Shugaban Kasa, kuma adadin dukiyarsa Dala biliyan 3 da digo 1 kuma babu wani abu da ya canja tun bara.

  • facebook
  • twitter
  • whatsapp
  • linkedin