Subscribe
  • facebook
  • twitter
  • whatsapp
  • linkedin
Na yi garkuwa da kaina ne don in je wurin saurayina – Budurwa

Kosisochukwu Anioma, wadda ta yi garkuwa da kanta

Na yi garkuwa da kaina ne don in je wurin saurayina – Budurwa

Rundunar ’Yan sandan Jihar Enugu ta gano wata budurwa da aka sanar da bacewarta, inda ta yi garkuwa da kanta ranar Alhamis da ta gabata don ta gudu wajen saurayinta.

Jami’an ’yan sandan da ke yaki da garkuwa da mutane ne suka gano inda budurwa take. A cewar Kakakin ’yan sandan Jihar Enugu Sufurtanda Ebere Amaraizu, budurwar da ake zargi da yin garkuwar bogin mai suna Kosisochukwu Anioma, mai shekara 14, ta amsa tuhumar da ’yan sandan ke yi mata, inda ta ce ta aikata  haka ne kawai don ta yi ido biyu da saurayinta wanda suka hadu a makaranta a Owerri babban birnin Jihar Imo.

Zuwa lokacin hada wannan rahoton, Kosisochukwu tana hannun ’yan sanda.  Budurwar ’yar wani dan siyasa ne a Jihar Enugu kuma Mataimaki na Musamman ga tsohon Gwamnan Jihar Mista Chimaroke Nnamani mai suna Frank Anioma.

Frank, ya sanar da rahoton bacewar ’yarsa Kosiso lokacin da ta tafi kasuwar New Haben.

“Na kira lambar wayar salular ’yata amma an ki amsa kiran, daga bisani sai wayar ta fara nuna alamar ana amfani da wayar sadarwar lokacin da nake kokarin kiranta,” inji Frank.

Bayan sanar da ’yan sanda ba tare da bata lokaci ba suka fara bincike daga nan suka samu nasarar gano inda Kosiso take a cikin garin Owerri.

A cewar Kakakin ’Yan sandan, Amaraizu, budurwa Kosiso ta amsa laifin yin garkuwa da kanta ne da nufin ta tafi zuwa garin Owerri don ganin saurayinta na makaranta.

Jami’an ’yan sandan sun bayyana cewa, budurwar da saurayin nata duk suna makarantar sakandare daya ne a garin Abakiliki, amma sai ta yanke shawarar ta je ta ga saurayin nata sakamakon dogon hutun da aka ba su, ta hanyar hilatar iyayenta cewa an yi garkuwa da ita.

Idan makarantar ta dawo hutu, Kosisochukwu da saurayinta dan garin Owerri za su shiga aji na hudu a makarantar sakandare, kamar yadda Kakakin ’Yan sandan ya sanar.