✕ CLOSE Noma Da Kiwo Hotuna Kiwon Lafiya Girke-Girke Sana'o'i Kimiyya da Kere-Kere Ra'ayin Aminiya Ra’ayoyi Rahoto
Click Here To Listen To Trust Radio Live

Na yi kokari wajen magance matsalar tsaro a Zamfara- Yari

Tsohon Gwamnan jihar Zamfara, Abdul’aziz Yari, a yau Litinin ya kare kansa game da kalubalen tsaro da jihar ke fuskanta, inda ya ce ya yi…

Tsohon Gwamnan jihar Zamfara, Abdul’aziz Yari, a yau Litinin ya kare kansa game da kalubalen tsaro da jihar ke fuskanta, inda ya ce ya yi bakin kokarinsa wajen magance matsalar tsaron da jihar ke fama da ita.

Majiyar Kamfanin Dillancin Labarai na Najeriya NAN ne bayyana haken, inda tsohon Gwamnan Zamfara ya sanar da hakan a garin Talata-Mafara wajen taron shugabannin jam’iyyar APC daga Kananan Hukumomin Gusau, Maradun da Tsafe.

Yari, ya kara da cewa, zai amfani da wannan damar wajen mika sakon ta’aziyyarsa ga jama’ar Maradun da Tsafe sakamakon harin da ‘yan bindiga suka kai unguwannin Kananan Hukumomin.  Kuma ya yi masu fatan Allah Ya gafartawa wadanda suka rasu, ya ba iyalansu hakurin jure rashin da aka yi.