✕ CLOSE Noma Da Kiwo Hotuna Kiwon Lafiya Girke-Girke Sana'o'i Kimiyya da Kere-Kere Ra'ayin Aminiya Ra’ayoyi Rahoto
Click Here To Listen To Trust Radio Live

Na yi murnar ban kamu da cutar Coronavirus ba – Iliyasu

Hukumar asibitin Gambo Sawaba da ke Kofar Gayan Zariya ta tabbatar da cewa, mutumin da ake zargin yana dauke da cutar Coronavirus mai suna Iliyasu…

Hukumar asibitin Gambo Sawaba da ke Kofar Gayan Zariya ta tabbatar da cewa, mutumin da ake zargin yana dauke da cutar Coronavirus mai suna Iliyasu Muktar bai kamu da cutar ba.

Iliyasu mai shekara 40 yana zaune ne a kauyen Dorayi da ke karamar hukumar Zariya jihar Kaduna, sakamakon gwajin da aka yi masa ya nuna bai kamu da cutar Coronavirus ba.

Hakan ya sa aka sallame shi daga asibitin, Babbar Daraktar Asibitin Dakta Hussaina Adamu ce ta shedawa Aminiya hakan a asibitin bayan sallamarsa.

Da yake nuna jin dadinsa Iliyasu Muktar, ya ce ya yi tafiya ne akan Babur na tsawon kwana uku daga Legas zuwa Zariya.

Dan haka sai ya yanke jiki ya fadi sakamakon dama baya jin dadi ya yi zazzabi a can garin Legas, faduwar da ya yi yasa aka yi masa zargin ya kamu da cutar COVID 19, daga nan aka fara kyamarsa tare da gudun duk wani danginsa.