✕ CLOSE Noma Da Kiwo Hotuna Kiwon Lafiya Girke-Girke Sana'o'i Kimiyya da Kere-Kere Ra'ayin Aminiya Ra’ayoyi Rahoto
Click Here To Listen To Trust Radio Live

Na yi tukin tasi na shekara 16 kafin na

zama farfesa – Dan takarar Gwamnan Borno A karon farko da zai bayyana wa duniya tarihinsa, dan takarar Gwamnan Jihar Borno a Jam’iyyar APC, Farfesa…

  • zama farfesa – Dan takarar Gwamnan Borno

A karon farko da zai bayyana wa duniya tarihinsa, dan takarar Gwamnan Jihar Borno a Jam’iyyar APC, Farfesa Babagana Umara Zulum ya bayyana wa Aminiya yadda ya taso daga wanda ba wani ba ne har zama wani. Babagana dai shi ne ya lashe zaben fid da gwani na Jam’iyyar APC domin tsayawa takarar Gwamnan Jihar Borno bisa irin goyon baya da ya samu daga Gwamnan Jihar Kashim Shettima.

Babagana wanda farfesa ne na Kimiyyar Noman Rani a Jami’ar Maiduguri a shirye yake ya fuskanci zaben na 2019.

Farfesa Babagana ya ce a tasowarsa ba zai yiwu ya zama malalaci ba domin ya taso ne a yanayin rayuwa da dole sai ya tashi ya nemi na kansa. Ya fara ne da tarihin gidansu, inda yake bin mahaifinsa su je aiki a gona tun yana karami a kauyen Loskuri da ke Karamar Hukumar Mafa a Jihar Borno.

“Kullum nakan taka a kafa na tsawon kilomita 7 zuwa gonar mahaifina,” inji shi.

Ya kasance yana hada zuwa gona da makaranta a lokacin yana makarantar firamare a Mafa da Mongunu a tsakanin 1980 da 1985, inda ya ce, tun daga aji biyar na sakandare, ya ci gaba da daukar nauyin karatunsa baki daya.

“Na yi tukin tasi musamman Fijo 404 a tsakanin 1984 zuwa kusan 1999, kimanin shekara 16 ke nan. Haka kuma na yi tukin bas, inda nake daukar fasinja zuwa kauyuka da wasu jihohi makwabta. Na kuma kasance direban babbar mota inda nake dakon itace daga daji. Sannan kuma lokacin da nake tukin, na koyi yadda ake gyara duk motar da na tuka.”

A 1986, Zulum ya samu gurbin karatu a Kwalejin Kimiyya da Kere-Kere ta Ramat da ke Maiduguri mallakar Gwamnatin Jihar Borno, inda ya yi Difloma a Kimiyyar Noman rani. Sannan lokacin da yake karatun yana zauna ne a gidan ’yan uwansu a Unguwar Kofa Biyu. “Na kasance ina tafiya ta tsawon kilomita 8 daga Kofa Biyu zuwa Kwalejin Ramat sannan in dawo duk ranar da nake da aji. Amma tun kafin nan na riga na saba da tafiya a kafa domin ba ni da kudin mota na zuwa makaranta. Duk lokacin da na yi aikin tuki, kudin da na tara nakan yi amfani da su ne wajen abubuwa masu muhimmanci ga karatuna. Daga baya kuma sai na hada  da yin nika a inji, inda na mallaki daya a Mafa, kuma duk karshen mako, nakan je can in yi nika ga abokan ciniki,” inji shi, inda ya ce a haka har ya samu shaidar difloma a 1988.

A 1989, Babagana ya samu aiki da Gwamnatin Jihar Borno a Ma’aikatar Gona ta Jihar. A s1990, sai ya koma Hukumar Kula da Kananan Hukomomi, “A lokacin da nake aiki, albashina bai iya daukar nauyina da wadanda suke karkashina. Don haka sai na ci gaba da tukin mota.”

Yana ci gaba da tukin ne har ya samu gurbin karatu a Jami’ar Maiduguri a 1990, inda ya kammala digiri a Kimiyyar Noma a 1994. Bayan shekara uku kuma, sai ya samu gurbin karatu a Jami’ar Ibadan inda ya yi digiri na biyu.

“Ba zan taba mantawa da abin da ya faru bayan na samu gurbin karatu a Jami’ar Ibadan ba domin yin digiri na biyu, domin sai da rashin kudi ya hana ni yin rajista har na dauki mako uku ban yi ba. Lokacin da na bar Maiduguri ba ni da kudi. Amma na yi imanin cewa zan samu wani dan aiki da zan yi a Legas da zan samu kudi. Na yi mako uku a Alabar Rago ina aikin tukin tasi  har na tara kudin makaranta. Sai na tafi Ibadan, na biya kudin makaranta, sannan na kammala a 1998, sannan na dawo na ci gaba da aiki a matsayin Babban Injiniyan Noma daga baya kuma na zama Babban Injiniyan Ruwa,” inji shi.

Babagana ya kara da cewa daga baya sai ya koma Jami’ar Maiduguri a matsayin karamin lakcara a jami’ar a 1998. Daga shekarar 2005 zuwa 2009 ya samu digiri na uku a Kimiyyar Ruwa da Kasa. Sannan ya taba zama Mataimakin Shugaban Tsangayar da kuma Mukaddashin Shugaban Tsangayar Kimiyyar Noma.

Babagana ya ci gaba da koyarwa duk da cewa ya samu mukami a gwamantin jihar a shekarar 2011. Sannan duk da cewa Gwamna Shettima ya zabe shi Shugaban Kwalejin Ramat a shekarar 2011, sai ya zabi ya ci gaba da karbar albashinsa na malamin jami’ar Maiduguri. Sannan ya ci gaba da koyar da dalibai a Jami’ar Maiduguri a daidai lokacin da yake Shugaban Kwalejin Ramat, “Ba na so wani abu ya dakatar da ni daga koyarwa a jami’a, don haka sai na ci gaba da rike koyarwa a jami’a a matsayin asalin aikina, sannan na ci gaba da yin sauran ayyuka ba tare da na tauye wani ba.”

A lokacin da yake Shugaban Kwalejin Ramat, Babagana ya jagoranci yin gine-gine manya a kwalejin ta hanyar amfani da kudin shiga da ake samu da kuma tallafi daga Gwamnatin Tarayya.

A shekarar 2015, sai Gwamna Shettima ya nada Babagana Zulum a matsayin Kwashina na farko na Ma’aikatar Sake Ginawa da Gyarawa  da Tsugunarwa, inda Gwamnan, ya shaida wa mutane a makonnjiya daya daga cikin abin da y jawo hankalinsa kan Babagana Zulum shi ne yadda duk da cewa akwai makudan kudade da suka kai biliyoyin Naira a karkashinsa da aka ware domin sake gina gidaje da makarantu da asibitoci da sauransu, “Bai saya wa kansa mota ba, kuma bai saya wa kansa gida da kudaden ba. Kuma Boko Haram sun kai masa hari sau biyu, amma duk da haka bai bar abin da ya sa a gaba ba.”

Shi ma Babagana Zulum da kansa ya tabbatar wa Aminiya cewa aikinsa a matsayin Kwamishinan Sake Gina Garuruwan shi ne aikin da ya fi shan wahala, “Gwamna Shettima ya fada min a watan Satumban 2015, cewa zai sanya kudade da yawa domin sake gina daruruwan garuruwa da Boko Haram suka barnata a karkashina, kuma ina alhinin yadda sama da mutum miliyan 2 suka bar garuruwansu,” inji shi.

“Wannan aikin ne mai wahala, sannan daga baya na dauki niyyar yin aikin ko dai in gama ko kuma in mutu a kai. A haka kuma wani lokacin akwai maganar tsaro domin ’yan ta’adda suna iya kawo hari a kowane lokaci, amma kuma mun samu cikakken tsaro da goyon baya daga sojoji da ’yan sanda da sauran jami’an tsaro da kuma ’yan sa-kai. Sake gina garuruwan abu ne da ya zama dole, domin Gwamnan ya ce ba zai yiwu mu yi ta jira ba. Ina matukar farin cikin yadda ya samu nasarar sake gina wasu garuruwa, musamman a yankin Bama. Yanzu gwamnati ta samu damar mayar da mutane garuruwansu a yawancin kananan hukomomi da suka hada da Bama da Kaga da Dikwa da Gwoza da Askira Uba da sauransu.

“Haka kuma mun samu damar gina sama da gidaje 10,000 a Bama da makarantu da asibitoci da sauran kananan hukomomin. Har yanzu ma’aikatar na ci gaba da aiki, kuma ina da tabbacin Gwamna zai kammala aikinsa na sake gina garuruwan, kuma wannan shi ne babban abin tarihi na Gwamnatin Gwamna Shettima da kuma mutanen Jihar Borno.”