✕ CLOSE Noma Da Kiwo Hotuna Kiwon Lafiya Girke-Girke Sana'o'i Kimiyya da Kere-Kere Ra'ayin Aminiya Ra’ayoyi Rahoto
Click Here To Listen To Trust Radio Live

Nadin Shugaban Tibi ya jawo zanga-zanga a Nasarawa

Kabilar Tibi da ke garin Agyaragu a Karamar Hukumar Obi a Jihar Nasarawa sun yi zanga-zanga dangane da nadin da Sarkin Migilli, Mista Ayuba Agwadu…

Kabilar Tibi da ke garin Agyaragu a Karamar Hukumar Obi a Jihar Nasarawa sun yi zanga-zanga dangane da nadin da Sarkin Migilli, Mista Ayuba Agwadu ya yi na mai unguwarsu a yankin.

Da yake zantawa da wakilinmu, wani dan kabilar Tibi, Mista Laurence Adaa ya ce nadin da aka yi wa Dogo Gberatse ya kawo rudani da rabuwar kawuna da rashin jituwa a tsakanin al’ummarsu a garin.

Ya ce al’ummarsu ta Tibi suna zabin masu unguwanninsu ne da kansu kamar yadda al’adarsu ta tanada, kuma a wannan karon ma sun zabi mutum biyu suka gabatar da su ga basaraken don ya tabbatar da daya daga cikinsu.

“Da farko Sarkin ya amince da su amma bayan wata uku sai ya gayyaci wadansu shugabannin al’ummarmu zuwa fadarsa, inda ya sanar da su cewa amincewar da ya yi da farko a kan wadanda aka zaba ya yi ne a kan kuskure. Daga baya sai ya nada Dogo Gberatse a matsayin mai unguwarmu a garin.

Saboda haka ba mu amince da wannan sabon salo na nada mana shugabanni da Sarki ke yi ba, don mu Tibi muna da namu hanyar nadi ko zaben shugabanninmu na gargajiya kamar yadda su ma Migilli suke da nasu salon zabin shugabanninsu. Kuma mutumin da ya nada shi mai unguwar ba asalin dan kabilar Tibi da ke nan ba ne, bako ne da ya fito daga wani waje daban. Shi ya sa muka fito kwanmu da kwarkwata muka nuna rashin amincewarmu da haka,” inji shi.

Wani fasto dan kabilar Tibi a garin mai suna Akuila Shinyi ya ce suna zamansu lafiya da juna da makwabtansu wadanda ba Tibi ba suna kuma yin biyayya ga dokokin masarautar ta Agyaragu kafin basaraken ya nada musu mai unguwa bayan sun zabi nasu sun gabatar masa da su.

“Yadda muke yi a tsarin zaben shugabanninmu na gargajiya kamar yadda al’adarmu ta tanada shi ne Tibi baki daya za su nada masu zaben shugabanni wadanda za su zaba mana shugabanninmu na gargajiya sannan su gabatar da su ga Sarkin Migilli don ya tabbatar da su. Mun bi dukan wadannan matakai mun kuma sanar da jami’an tsaro na yankin nan game da zaben wadannan masu unguwannin namu muka kuma sanar da su cewa nan ba da dadewa ba za mu yi musu wankar sarauta. Muna shirin yin haka ne sai kawai Sarki ya umarci a dakatar da mu cewa garin baki daya yana cikin rudani dangane da bikin.

Amma a bangarenmu ba mu da wata matsala da bikin. Daga bisani ne muka fahimci cewa manufarsa ita ce ya maye gurbin wadanda muka zaba da wanda yake so a kujerar inda ya nada wannan bakon a wannan matsayi. Shi ya sa muke korafi cewa nadinsa ya sha bamban da tanadin al’adarmu. Saboda haka muna kira ga Mai martaba Sarki ya sake tunani ya ba mu damar zaben shugabanninmu na gargajiya kamar yadda ake yi a dukan garuruwa da kauyukan al’ummar Tibi a fadin jihar nan don ci gaba da samun zaman lafiya a garin nan,” inji Faston.

Kokarin da wakilinmu ya yi don jin ta bakin Sarkin na Migilli dangane da batun ya ci tura, domin sau da yawa wakilinmu yana tafiya fadarsa ba ya samunsa.