Hukumar Jindadin Alhazan Najeriya ta Kasa (NAHCON) a yau Asabar ta soma jigilar Alhazai zuwa gida Najeriya bayan kammala aiki hajin bana.
Hukumar tun farko ta sanar da yau a matsayin ranar fara jigilar Alhazai zuwa gida Najeriya.
An soma yin jigilar ne da alhazan jihar Legas su 432 a jirgin Flynas mai lamba XY7434 wanda ya taso daga filin jirgin sama na Sarki Abdulaziz da ke Jeddah.
A cewar sanarwa daga sashen kula da jigila na Hukumar NAHCON, jirgin ya baro kasar Saudiya ne zuwa Najeriya da misalin karfe 3 na kasar watau karfe 1 kenan a Najeriya.
Kuma ana sa ran isowar Alhazan gida Najeriya watau na jihar Legas da misalin karfe 6 na yammancin yau.