✕ CLOSE Noma Da Kiwo Hotuna Kiwon Lafiya Girke-Girke Sana'o'i Kimiyya da Kere-Kere Ra'ayin Aminiya Ra’ayoyi Rahoto
Click Here To Listen To Trust Radio Live

NAHCON ta yabawa al’hazan Kaduna a kasar Saudiya

Shugaban Hukumar Hajji ta Kasa  (NAHCON), Barista Abdullahi Muktar ya yaba wa alhazan Jihar Kaduna bisa yadda suke hakuri tare da biyayya ga shugabaninsu a…

Shugaban Hukumar Hajji ta Kasa  (NAHCON), Barista Abdullahi Muktar ya yaba wa alhazan Jihar Kaduna bisa yadda suke hakuri tare da biyayya ga shugabaninsu a Kasa Mai tsarki.

Shugaban ya bayyana haka ne lokacin da ya kai ziyara heman alhazan Jihar Kaduna da ke Mina a daren Talatar da ta gabata.

Ya ce duk da kalubale da alhazan suke fuskanta amma suna ci gaba da yin hakuri tare da mayar da hankalinsu wajen gudanar da ibadarsu cikin kwanciyar hankali.

Barista Mukhtar ya shawarce su kan su ci gaba da kasancewa jakadun Najeriya nagari a kasar Saudiyya tare da tabbatar musu da cewa Hukumar NAHCON da Hukumar Jin Dadin Alhazan Jihar za su ci gaba da yin iya kokarinsu wajen inganta jin dadinsu har zuwa lokacin da za su koma gida Najeriya.

A wata sabuwa kuma, Shugabar Kwamitin Kula da Ciyar da Alhazai ta Jihar Kaduna Hajiya Hadiza Yahaya ta ce a bana sun samu ci gaba wajen ciyar da alhazan jihar a kasar Saudiyya.

Kakakin Hukumar Jin Dadin Alhazan Jihar Kaduna, Malam Yunusa Abdullahi ne ya sanar da haka a wata sanarwa da ya fitar ga manema labarai.

A cewarta, yanzu haka wasu jihohi shida sun yi koyi da salon jadawalin rabon abinci da jihar ta yi amfani da  shi domin inganta jin dadin alhazanta.

Shugabar ta bayyana cewa a shirye suke su karbi shawarwari domin inganta tsarin da suke bi a yanzu domin kara saukakawa da inganta jin dadin alhazan.

“A wajen rabon abinci muna bukatar jajircewa matuka kuma a bana mun yi amfani da jadawalin da ya saukaka mana aiki wanda har ta kai ga wasu jihohi suna koyi da Jihar Kaduna,” inji ta.