✕ CLOSE Noma Da Kiwo Hotuna Kiwon Lafiya Girke-Girke Sana'o'i Kimiyya da Kere-Kere Ra'ayin Aminiya Ra’ayoyi Rahoto
Click Here To Listen To Trust Radio Live

‘Naira dubu 500 aka ba mu mu kashe Sheikh Sani Yahaya Jingir’

Maharan da suka kitsa harin bam a Jos da Zariya sun ce an biya su Naira dubu 500 ne domin su kashe Shugaban Majalisar Malamai…

Maharan da suka kitsa harin bam a Jos da Zariya sun ce an biya su Naira dubu 500 ne domin su kashe Shugaban Majalisar Malamai ta kungiyar Jama’atu Izalatil Bidi’ah Wa Ikamatis Sunnah ta kasa Sheikh Muhammad Sani Yahaya Jingir.

Maharan sun bayyana haka ne jim kadan da kama su da jami’an tsaro suka yi a shekarnjiya Laraba a Dadin Kowa da ke Jihar Gombe, kamar yadda ke kunshe a wani faifai da ya fara yawo a kafofin sadarwa na Intanet.
daya daga cikin maharan ya ce: “Wani mai suna Ali da ke cikin Dajin Sambisa ne ya ce mu je mu kashe Yahaya Jingir kuma ya ba mu Naira dubu 500, amma Abubakar shi ne ya san komai a cikinmu, mun je da bam da kuma bindiga amma mai bindigar ya mutu.”
Shi kuwa direbansu ya ce bai san komai ba game da batun, an dai an ba shi Naira dubu 10 aka ce ya kai su Jos da Zariya idan suka kammala abin da za su yi, ya dawo da su ya sauke su a inda ya dauke su, wato kan hanyar shiga Maiduguri.
Sai dai daya daga cikin maharan ya karyata direban nasu, inda ya ce babu abin da bai sani ba, domin tare suke aiwatar da komai da shi.
Shugaban nasu mai suna Abubukar bai samu damar furta komai ba, saboda raunin da aka yi masaa kafa a dalilin harbin bindiga.
Sojoji sun kama maharan ne tare da hadin gwiwar jami’an tsaro na SSS a garin Dadin Kowa da ke Jihar Gombe a wani shingen binciken ababen hawa.
Harin bindigogi da bama-bamai a Masallacin ’Yan Taya da ke titin Dilimi dab da hanyar Bauchi Road da wanda aka kai a shagon sayar da abinci na Hajiya Talatu Shagalinku da ke titin Bauchi Road duk a garin Jos ya hallaka mutum 48 tare da raunata da dama. Sai kuma na Zariya, inda sama da mutum 30 suka rasu lokacin da ake tantance ma’aikata a Sakatariyar karamar Hukumar Sabon Gari.
Duk da cewa Kakakin Sojojin Najeriya Kanar Sani Usman Kukasheka ne ya bayar da sanarwar kamun, wata majiya ta ce Hukumar DSS a karkashin jagorancin Lawal Daura ne ta yi kamun.