✕ CLOSE Noma Da Kiwo Hotuna Kiwon Lafiya Girke-Girke Sana'o'i Kimiyya da Kere-Kere Ra'ayin Aminiya Ra’ayoyi Rahoto
Click Here To Listen To Trust Radio Live

NAJERIYA A YAU: Ma’aikatar Shari’a ta fadi gwajin tsare gaskiya —ICPC

Yadda hukumomin Gwamnatin Tarayya 124 suka gaza a gwajin da’a, tsare gaskiya da bin ka’idojin aikin

More Podcasts

Domin saukewa latsa nan 

Yaya za ka yi a lokacin da kake neman a kwato maka hakkinka, amma ka ji gwamnati na cewa Ma’aikatar Shari’a ta fadi gwajin tsare gaskiya. 

Kun san cewa hukumomi da Ma’aikatun Gwamnatin Tarayya 124 ne suka gaza a gwajin da’a, tsare gaskiya da bin ka’idar aiki da hukumar yaki da laifukan zamba da dangoginsu (ICPC) ta gudanar?

Ma’aikatar Shari’a, hukumar ’yan sanda da Babbat Kotun Tarayya ta kasa na daga cikin wadanda suka fadi warwas; A yayin da wasu 52 suka ki yarda ICPC ta yi musu gwajin.

Shirin Najeriya a yau ya tattauna da masu ruwa da tsaki da kuma masana don fayyace mana yadda al’amarin yake.