✕ CLOSE Noma Da Kiwo Hotuna Kiwon Lafiya Girke-Girke Sana'o'i Kimiyya da Kere-Kere Ra'ayin Aminiya Ra’ayoyi Rahoto
Click Here To Listen To Trust Radio Live

Najeriya ce a gaba ba Buhari ba

Rajistar da aka yi wa jam’iyyar APC, wadda hadaka ce ta jam’iyyun kasar nan, al’amari ne da ya haifar da matukar farin ciki da samun…

Rajistar da aka yi wa jam’iyyar APC, wadda hadaka ce ta jam’iyyun kasar nan, al’amari ne da ya haifar da matukar farin ciki da samun kwarin gwiwar karfafa dimokuradiyya, tare da fatan kai ga gaci ga kasar mu, a lokacin da kasa ta yanke kauna. Wannan abin da aka yi kawai, shugabannin jam’iyyun adawa da suka yi hadaka, sun yi nuni da cewa Najeriya na da makoma, tare da samun ci gaba da walwalar al’ummarta su ne ke da fifiko a kan burin wani mutum kwal. Don haka Jam’iyyar APC matakin takawa ce (dandali ne) da ’yan Najeriya za su hau, wajen neman sauyi da cikar burinsu, a cikin kakkarfar jam’iyya da ta karade fadin kasar. karin haske a kan haka, shi ne ta yunkuro don kawar da danniya da yamutsin rashin bin doka da oda.
Dimokuradiyya ba wai ta takaita a kan zabe mai inganci ba ne, ko kuma salo da dabarun da jam’iyyu ke bi wajen kafa gwamnatoci. Tana ma samar da damarmaki wajen aiwatar da sababbin tsare-tsare da za su ciyar da kasa gaba. Don haka ne tsarin shugaba mai cikakken iko ke da wa’adinsa, tamkar yadda muke yi a nan, amma yunkurin karin wa’adin mulki a karo na uku da aka taba bijiro da shi, wanda bai samu nasara ba, alamu ne da ke nuni da cewa, wasu ’yan siyasar idan aka ba su dama sai su rusa tsarin da ake kai. A tsarin Firayiminista kuwa, inda ba a gindaya wa’adi ba, shugabannin jam’iyyu za su iya cire shugaban gwamnati, kowace irin nasara ya/ta samu da kuma irin farin jinin da ya/take da shi a wajen masu kada kuri’a. Wannan ita ce makomar Firayiministocin Birtaniya biyu, wato Margret Thatcher da Tony Blair, a ’yan shekarun nan. Sauyi mafi sauki, shi ne, idan aka bayar da damar yin zabe mai inganci, masu kada kuri’a za su iya kawar da gwamnatin da ba ta da tagomashi, tamfar abin da ya faru ga Misis Ghandi a kasar Indiya.
Hadarin da ke tattare da bin tafarkin jam’iyya guda ko kuma wani mutum daya kwal ya yi ta jan ragamar mulki na tsawon lokaci, ribi biyu ne: yaudara zakin mulki; domin an sha yin nuni da cewa karfin mulki  kan gurbata (tunanin) mai rike da madafun iko. Al’amari na biyu kuwa shi ne ruduwa da son kankame komai, don haka mulkin jam’iyya daya kan iya haifar da mulkin wani rukuni na ’yan jam’iyyar, kuma tabbas shi ne mulkin mutum guda, tamkar yadda mulkin kasa (Rasha) ya kasance a karakashin Stalin.
Abin takaici shi ne, bayan an yi kwarya-kwaryar farin cikin samun rajista, takaddamar da ake ta yi a tsakanin al’umma duk ta ta’allaka a kan wasu manyan mutane, fiye da karkata akalar tunani wajen dimbin alfanun da ke tattare da managarciyar damar samun sauyi daga hannun jam’iyya mai mulki, da kuma hanyoyin bunkasa dimokuradiyya, ta yadda za a kauce wa keta haddin doka, inda zababben shugaba ke nuna ko in kula kan abin da ke damun al’umma.
Wannan al’amari dai ba abin da ya shafi buhari shi kadai ba ne, domin wani lamari ne da ke da girma fiye da Buhari ko wani mutum shi kadai ko wasu sassa, wato makomar Najeriya ce a gaba da ci gabanta da walwalar al’ummarta, ta yadda za su zauna cikin kwanciyar hankali da juna, inda za a, a hade wuri guda don daukaka kimar darajarta.
Shigata aikin soja, sadaukar da rayuwata ce ga kasata. Wannan shi ne al’amarin da ni da abokaina muka fuskanta a lokacin mummunan yakin basasar da aka fafata da manufar tabbatar da kasarmu a matsayin dunkulalliyar kasa daya. Najeriya ta kyautata mini. Ni maraya ne, amma ta ilimantar da ni, ta horar da ni, sannan ta ba ni babban matsayi da kowane dan kasa kan yi fatan kai wa gare shi.
shigata cikin harkokin siyasa nema na aka yi in bayar da gudunmuwa, tare da burina na bai wa Najeriya dan irin tallafin da zan iya bata, daga cikin abin da ta ba ni, ta hanyar hada karfi da wasu don samar da hanyar kwakkwara ga ’yan kasa, wajen kawo sauyin inganta zamantakewa da managartan tsare-tsaren tattalin arziki, wadanda za su dore wajen jawo kowa a jika a tafi tare, ta hanyar kafa jagoranci da ya himmatu wajen  inganta tattalin arziki da tabbatar da adalci a zamantakewa da ’yanci.
Irin wannan jagoranci bai ta’allaka ga gwamnati kawai ba, domin duk muna da gudunmuwar da za mu iya bayarwa, ta yadda Majalisar kasa da Hukumar shari’a da jami’an tsaro da kafafen yada labarai da kungiyoyin fafutikar hakkin dan Adam, za su bibiyi kadin gaskiyar abin da ake aiwatarwa, tare da bayar da kariya ga kowa da kowa a karkashin doka, inda za a rika bayyana gaskiya karara.
Idan wasu ’yan siyasana ganin wata dabara ce su karkata akalar muhawara kan gazawar Najeriya, don dauke hankalin mutane daga nakasunsu, su kuma kawar da hankali daga irin satar dukiyar al’umma da suke yi, nauyi ya rataya akan ’yan jarida su juya akalar takaddamar ce ce ku ce kan sare-tsare da ayyukan da ake aiwatarwa, ba tare da la’akari da dabaru dauke hankali daga salon batanci da illar da Jam’iyyar PDP ta yi wa kanta ba.
Buhari, tsohon Shugaban kasa ne, kuma jigo ne a Jam’iyyar APC.