Da Dumi Dumi

Najeriya ce kan gaba wajen samar da doya a duniya – Audu Ogbeh

Gwamantin Tarayya ta bayyana cewa ba za ta yi wasa da batun shirinta na fitar da doya zuwa ga kasuwannin duniya don cigaba da jawo hankalin masu zuba jari tare kuma da farfado da darajar naira ba. Kasancewar Najeriya ce kasa mafi girma wajen yawan samar da doya a duniya. Saboda mu ke samar da doya kashi 67 cikin 100 na yawan doyar da duniya ke samarwa. 

Ministan Harkokin Noma da Raya Karkara, Cif Audu Ogbeh ne ya bayyana haka a yayin tattakin wayar da kan jama’a da aka gudanar a ranar Abinci na Duniya a Abuja ranar Talatar da ta gabata kamar yadda Kamfanin Dillancin Labarai na Najeriya (NAN) ya ruwaito. 

Cif Audu Ogbeh, ya yi wannan faruci a matsayin martini kan rahotannin dake ci gaba da bayyana cewa doyar da Najeriyar ta fitar kwanan nan zuwa kasar Birtaniya ya gaza samun tagomashin da ya dace, yana mai cewa wannan shiri na nan daram.

Ministan ya ci gaba da cewa, wannan makarkashiya ba za ta girgiza gwamnatin tarayya ba, sannan kuma ba za ta yi tasiri wajen kashe gwiwar manyan ‘yan kasuwarmu da masu noman doya a kasar nan daga fita da ita zuwa kasuwannin duniya ba. Ya kuma kara da cewa a yanzu haka kasuwar doyar a kasuwannin duniyar ta haura dala biliyan 12.

ADVERTISEMENT

Ministan ya kara da cewa ko kadan kasar ba za ta lamunci yin watsi da wannan babbar harkar ba, domin Najeriya ce kasar da ta fi kowacce yawan samar da doya a duniya. “Hakika na samu wasu labaran dake nuni da cewa wai Najeriya ta fitar da doya zuwa Birtaniya, amma wai an ki amincewa da ita. Idan hakan ta faru, to doyar ce ta jima a ajiye, ita kuwa doya ba ta jima lalacewa ko ta rube, amma ba wai don rashin kyan doyar ba.”

“Kuma hakan ta faru ga kasar Ghana ma. Don haka ba zamu yi watsi da shirin fitar da doya ba. Ina mai tabbatar maku cewa, wannan shiri ne tabbatacce kasancewar Najeriya ce kasa mafi girma wajen yawan samar da doya a duniya. Saboda mu ke samar da doya kashi 67 cikin 100 na yawan doyar da duniya ke samarwa.”

“Don haka zamu cigaba da karfafa gwiwar masu fita da ita zuwa kasuwannin duniya, koda yake ba kasar ce ke da masana’antun samar da doya ba, amma za ta cigaba da tallafawa kamfanonin ‘yan kasuwa don kaiwa gaci, kuma duk sadda aka samu wata matsala zamu magance ta,” a cewarsa. 

Kamfanin Labaran na (NAN) ya ruwaito cewa gwamnatin tarayya ta kaddamar da wannan shiri na karfafa fitar da doya daga kasar zuwa kasuwannin duniya ne a Watan Yunin bana, amma wasu manyan ‘yan kusuwar sun bayyana cewa akwai matsaloli da suka dabaibaye harkar safarar doyar zuwa kasuwannanin duniyar, sannan suka bukaci gwamnatin tarayya shigo don magance ta, tab yadda zasu samu saukin kasuwancin nasu yadda ya kamata.

Share