✕ CLOSE Noma Da Kiwo Hotuna Kiwon Lafiya Girke-Girke Sana'o'i Kimiyya da Kere-Kere Ra'ayin Aminiya Ra’ayoyi Rahoto
Click Here To Listen To Trust Radio Live

Najeriya na cikin kasashen da za su biya kudin garkuwa kafin su shiga Birtaniya

kasar Birtaniya za ta rika karbar kudin garkuwa ga al’ummar kasashen da ta yi wa mulkin mallaka, in data bayyana kasashe shida, wadanda suka hada…

kasar Birtaniya za ta rika karbar kudin garkuwa ga al’ummar kasashen da ta yi wa mulkin mallaka, in data bayyana kasashe shida, wadanda suka hada har da Najeriya da Bangladesh da Pakistan da Ghana da Sri lanka da Indiya. An bullo da karbar wannan kudi na garkuwa, wanda kimarsu ya kai Fam dubu uku, don haka bakin haure shiga kasar, ko kuma wadanda izinin zamansu ya kare, su samu damar ci gaba da zama.
A wani sakon i-mail da Kamfanin dillancin Labarai na AP ya baza, an bayyana cewa, wannan doka ta kudin garkuwa, zai shafi al’umma kasashen da suke da yawan mutanen da izinin shiga kasarsu ya kare, amma suka ci gaba da zama; da kuma bakin haure. Duk kuma wanda ya wuce ka’idar wa’adin da aka debar masa, to zai yi asarar wadannan kudi.
Hukumomin Birtaniya sun tabbatar da wannan rahoton, inda suka bayyana cewa kudin garkuwar Fam dubu uku ne a kan kowane mai kai ziyara kasar, matukar ya fito daga kasashe shida da aka lissafa. Ministan Harkokin Wajen Najeriya, Olugbenga Ashiru ya kirawo Jakadan Birtaniya a Najeriya, inda ya nuna rashin jin dadinsa kan wannan wariya da aka nuna musu.