✕ CLOSE Noma Da Kiwo Hotuna Kiwon Lafiya Girke-Girke Sana'o'i Kimiyya da Kere-Kere Ra'ayin Aminiya Ra’ayoyi Rahoto
Click Here To Listen To Trust Radio Live

Najeriya ta gano hanyoyin kudaden shiga 22 da za su maye gurbin man fetur

An bayyana hanyoyi 22 da Gwamnatin Tarayya za ta iya samun kudaden shiga wadanda za su iya maye gurbin kudaden da ake samu ta hanyar…

An bayyana hanyoyi 22 da Gwamnatin Tarayya za ta iya samun kudaden shiga wadanda za su iya maye gurbin kudaden da ake samu ta hanyar cinikin danyen man fetur a kasuwannin duniya.

Jaridar Premium Times ta ruwaito cewa; Shugaban Hukumar Karfafa Kayan Kasuwanci zuwa Waje, Mista Segun Awolowo ne ya bayyana haka.

Miste Segun Awolowo ya yi wannan bayani ne a ranar Juma’ar da ta gabata ga manema labarai na Fadar Shugaban Kasa, jim kadan bayan kammala ganawar da ya yi da Shugaba Muhammadu Buhari.

Sai dai kuma Awolowo bai bayyana wa manema labarai wadannan hanyoyi 22 da ya bugi kirji da su ba.

Amma dai ya shaida musu cewa ya fayyace wa Shugaban Kasa hanyoyin da za a bi domin fadada tattalin arzikin kasa ta hanyar kara samun makudan kudaden shiga. Ya ce dukkan abin da ya shaida masa, suna cikin tsarin da kwamitin fadada tattalin arziki da Majalisar Tattalin Arziki ta Kasa ta kafa.

An kafa wannan kwamiti na musamman ne a karkashin shugabancin Gwamnan Jihar Jigawa, Alhaji Badaru Abubakar. Kuma an dora masa alhakin lalubo hanyoyin samun kudaden shiga wadanda ba na man fetur ba.

Cif Awolowo ya kara da cewa duk da farashin danyen mai ya kara kudi a kwanan nan, kuma danyen man shi ne kashi 90 bisa 100 na hanyar samun kudin shiga ga Najeriya, Najeriya ba za ta iya dogara da danyen man fetur shi kadai ba. Ya ce tilas sai an nemo wasu hanyoyin samun kudin shiga domin inganta tattalin arzikin kasar nan.

“Tilas sai gwamnati ta kara lalubo hanyoyin samun kudaden shiga. Domin lokacin da farashin gangar danyen man fetur ke kai Dala 140, ya shude, har abada an wuce wurin. Don haka tilas sai mun kara nemo wasu hanyoyin samun kudade,” inji Awolowo.

“Muna da wasu hanyoyi 22 na samun kudaden shiga ga Gwamnatin Tarayya, ba tare da dogaro da danyen mai ba. Don haka muna fata nan da shekara 10-15. Za mu iya samun akalla Dala bilyan 150 daga wasu hanyoyin kudaden shiga da ba na man fetur ba,” inji shi.

Wasu daga cikin hanyoyi da Awolowo ya bayyana, akwai shirin Babbban Bankin Najeriya (CBN) na bayar da lamuni ga manoman da za su rika noma kayan amfanin gona na kasuwanci irin su koko da yazawa da tumatur da sauransu.