✕ CLOSE Noma Da Kiwo Hotuna Kiwon Lafiya Girke-Girke Sana'o'i Kimiyya da Kere-Kere Ra'ayin Aminiya Ra’ayoyi Rahoto
Click Here To Listen To Trust Radio Live

Najeriya ta shiga kwamitin tattalin arziki na Majalisar Dinkin Duniya

Babban Zauren Majalisar Dinkin Duniya ya zabi Najeriya da wasu kasashe 17 a matsayin mambobi a Kwamitin Tattalin Arziki na majalisar ranar Laraba. Kamfanin Dillancin…

Babban Zauren Majalisar Dinkin Duniya ya zabi Najeriya da wasu kasashe 17 a matsayin mambobi a Kwamitin Tattalin Arziki na majalisar ranar Laraba.

Kamfanin Dillancin Labaran Najeriya (NAN) ya rawaito cewa wa’adin sababbin mambobin kasashen zai fara ne daga ranar 1 ga watan Janairun 2021 kuma zai kasance na tsawon shekaru uku.

Wannan dai shi ne karo na uku da Najeriya za ta kasance mamba a wannan muhimmin kwamitin tun shekara ta 2012.

Kwamitin, wanda ke zama ruhin majalisar shi ne yake da alhakin juya akalar harkokin tattalin arziki, walwalar jama’a da kuma batutuwan da suka shafi muhalli na Majalisar.

A yayin zaben na ranar Laraba dai gurabe 14 ne aka ware wa kasashen Afirka, ragowar kujeru biyar ne kacal kuma aka fafata a kansu.

Kasashen da aka zaba

Kasashen Madagascar, da Laberiya, da Libya, da Zimbabwe da kuma Najeriya ne aka zaba bayan sun sami amincewar kungiyoyin yankunan da suka fito tun da farko.

Sauran kasashen da aka zaba sun hada da Indonesia, da Japan da kuma tsibiran Solomon wadanda za su wakilci nahiyar Asiya da kasashen Fasifik.

Sauran su ne kasashen Argentina, da Bolivia, da Guatemala da kuma Mexico wadanda za su wakilci Latin Amurka da yankin Caribbean.

Daga nahiyar Turai kuwa, kasashen Austria, da Faransa, da Jamus, da Portugal da kuma Ingila ne za su cike gurabun kujeru biyar daga yankin.

Muhimmancin Najeriya

Mataimakin Jakadan Najeriya a zauren, Mista Samson Itegboje, ya shaida wa NAN cewa sake zaben kasar shekaru biyu kacal bayan kammala wa’adinta na baya na nuna irin muhimmancinta a harkar diflomasiyya a Majalisar.

A kan dalilin ya sa yake ganin kasancewa mamba na da muhimmanci ga Najeriya, Mista Itegboje ya ce kwamitin wani ginshiki ne a Majalisar.

Ya ce a tsarin gudanar da Majalisar, kwamitin ne ke da alhakin bunkasa walwalar jama’a, samar da ayyukan yi da kuma habaka tattalin arzikin kasashe.

Ya lura cewa kasancewar Najeriya mamba a kwamitin zai taimaka mata wajen tallata manufofinta da ma na sauran kasashen Afirka a zauren.