Subscribe
  • facebook
  • twitter
  • whatsapp
  • linkedin
Najeriya za ta amfana sosai da yarjejeniyar kasuwanci ta Afirka  idan … Yusha’u Aliyu

Shugabannin kasashen Afirka a yayin taron kulla yarjejeniyar kasuwanci ta Afirka a Jamhuriyyar Nijar

Najeriya za ta amfana sosai da yarjejeniyar kasuwanci ta Afirka  idan … Yusha’u Aliyu

A ranar Lahadin da ta gabata ce Najeriya ta shiga sahun kasashe 54 daga cikin 55 na Nahiyar Afirka da suka rattaba hannu kan yarjejeniyar kasuwanci da za ta samar da kasuwar bai- daya a nahiyar.

Tsarin kamar yadda jagororin aiwatar da shi suka yi bayani, zai kawo karshen shingen da ke kawo cikas ga hada-hadar kasuwanci ko zirga-zirga a tsakanin al’ummar nahiyar.

Taron wanda ya kasance na yini hudu da ya shafi tattaunawa a tsakanin jagororin wasu ma’aikatun gwamnati, daga bisani shugabannin kasashen, ya gudana ne a Yamai babban birnin Jamhuriyar Nijar kuma kusan dukkan shugabannin kasashen nahiyar sun halarci taron. Haka akwai wakilai daga Majalisar Dinkin Duniya da Tarayyar Turai, sai kuma jagororin wasu kungiyoyin ’yan kasuwa da na fafutikar kare hakkokin jama’a daga nahiyar.

A jawabin da ya gabatar bayan rattaba hannu a kan yarjejeniyar da ake kira “AFCFTA” a takaice, Shugaban Kasa Muhammadu Buhari ya ce Najeriya za ta tabbatar da amincewarta a kan yarjejeniyar, wajen tabbatar da wanzuwarsa da aka tsara za a fara aiwatar da shi a badi.

Shugaba Buhari, wanda ya yi fatar yarjejeniyar za ta kawo dimbin ayyukan yi ga matasan Afirka da wadansunsu ke kasadar ficewa zuwa wasu nahiyoyin a kullum wajen neman abin yi, ya ce kasar nan za ta yi amfani da matsayinta na jagaba a nahiyar wajen ganin tabbatuwar nasarar yarjejeniyar, wadda hedikwatarta za ta kasance a kasar Ghana da ke Afirka ta Yamma.

Aminiya ta tuntubi wani masanin tattalin arzikin kasa, Malam Yusha’u Aliyu, wanda ya ce Najeriya na iya kasancewa a gaba wajen cin gajiyar tsarin fiye da kowace kasa a nahiyar bisa la’akari da yawan al’ummarta matukar ta shirya wa lamarin. Ya ce a farkon fara amfani da tsarin za a zabge kashi 90 cikin 100 na harajin da ake karba wajen shiga da haja daga wata kasa zuwa wata a tsakanin kasashen nahiyar 55, in ban da kasar Eriteriya da ba ta sa hannu ba zuwa lokacin kare taron.

Malam Yusha’u Aliyu ya ce Nahiyar Afirka na da karfin arzikin kasuwanci na Dala tiriliyan 7, inda kashi 40 cikin al’ummarta biliyan 1 da miliyan 200 ke hada-hadar Dala tiriliyan 4  duk shekara, kuma shi ne kasuwanci mai girma a duniya. Ya ce an yi hasashen cewa tattalin arzikin zai samu karin tagomashin kashi 56 cikin 100 nan da shekarar 2022, lokacin da za a sake waiwayar yarjejeniyar bayan fara aiki da ita a badi.

Yusha’u Aliyu ya ce tsarin yana da burin cimma ajandoji 3 da suka hada da habaka tattalin arziki da musayar kimiyya a tsakanin kasashe, sai tsarin bai-daya na tattalin arziki.

Najeriya da wasu kasashe da suka fi girman tattalin arziki a nahiyar kamarAfirka ta Kudu sun yi jinkirin shiga yarjejeniyar ce don gudun fadawa tsakiyar ruwa, bayan kiraye-keraye daga masana tattalin arzikin kasashen na a guji shiga yarjejeniyoyin kasuwanci cikin gaggawa, har sai masana sun tantace tukuna.

Haka nan ya ce Shugaban Kasa Muhammadu Buhari ya saurari korafin wasu kungiyoyin ’yan kasuwar Najeriya inda hakan ya jawo tsaiko wajen sanya wa yarjejeniyar hannu, bayan sun nuna rashin amincewarsu da tsarin, kuma a dalilin haka aka kafa wani kwamitin shugabannin kasashen da ’yan kasuwar a ciki; don sauraron koke-kokensu da kuma yadda za a tsare musu ’yancinsu a nan Najeriya da sauran kasashen nahiyar.

Ya ce tsarin da Turawan mulkin mallaka suka bar Nahiyar Afirka a kai shi ne, na a samar musu da sinadaran raya masana’antunsu, inda manoman Afirka da mahaka ma’adinanta ko sassakarsa za su samar da abin sarrafawa a masana’antun da ke kasashensu da wasu daga cikin matasan Afirka ke matsayin leburori a wurin. Sannan bayan an sarrafa kuma sai a sake dawo da kayan zuwa Afirka a matsayin nasu, a sayar. Ya ce a tsarin na AFCFTA da ake so  gudanarwa, shi ne a sauya hakan.

Ya hori Gwamnatin Tarayya ta tallafa wa daukacin bangarorin sana’a da suka hada da noma da hakar ma’adinai ko gyara shi ta hanyar ba da horon dabarun zamani da kayan aiki kan tsarin rance, tare da tallafa wa masana’antun da za su sarrafa abubuwan da suke samarwa zuwa wani mataki, maimakon fita da su zuwa wasu kasashe a matakin sinadari kawai.

Sai dai ya ce hakan ba zai samu nasara ba sai su kansu masu sana’o’in sun kakkafa kungiyoyi da tsara yadda za su kafa kananan masana’antu, sannan gwamnati a nata bangaren ta kafa bankuna kamar uku da suka hada da na manoma da sauran masu sana’a, da shigo da Bankin CBN cikin lamarin, sai kuma Bankin Afirka.

Malam Yusha’u Aliyu
Malam Yusha’u Aliyu

Ya ce dole ne a hada kai da wasu jami’o’in kimiyya da kere-kere wadanda za su rika kirkiro fasaha ta dindindin don samar da jagororin tafiyar da masana’antun da jawo kungiyoyin sa-kai da za su rika fadakarwa. Masanin tattalin arzikin ya kuma bukaci gwamnati ta kara wa hukumarta ta tabbatar da ingancin kayan masana’antu (SON), karfi ta hanyar daukar isassun ma’aikata don sa ido a kan abubuwan da za a rika yi, ta yadda duk inda kayan kasar nan ya je a nahiyar za a dauke shi a matsayin mai inganci don samun karbuwa.

“Dole kuma a ilimantar da al’ummammu a harkar tallata haja ta Intanet da kasashe irin su Kenya suka yi nisa a kai. Muna da damar cin moriyar tsarin fiye da kowace kasa, kasancewar a cikin mutum biliyan 1 da miliyan 200 da ke Nahiyar Afirka, ko mutum miliyan 385 da ke Afirka ta Yamma, Najeriya kadai na da mutum miliyan 200 daga cikinsu.

“Idan muka inganta kayanmu sannan gwamnati ta taimaka, yana iya sayuwa a farashi mai sauki, za mu fi kowace kasa a nahiyar ciniki saboda yawanmu kawai. Sai dai fa idan aka samu akasi, to kasarmu za ta zamo matattarar hajar kowace kasa a nahiyar; kasancewarta ita ce mafi girman kasuwa a Afirka,” inji shi.

Haka ya ce dole gwamnati ta samar da karin jami’an tsaro a kan iyaka da kuma sama masu cikakken kayan aiki don tabbatar da cewa ba a shigo wa kasar nan da makamai ko miyagun kwayoyi ba ko safarar jama’a marasa aikin yi.

“Haka nan kasashen da suka ci gaba za su sa ido wajen ganin sun yi shigar burtu, ta hanyar amfani da wasu al’ummarmu wajen shigowa da kayansu don ganin ba su biya haraji ba,” inji malam Yusha’u Aliyu.

Ya ce nada mutum guda ya shugabanci daukacin bangarorin uku da kowannensu ke matsayin babban waje, ba karamin kuskure ba ne.

Sai dai ya ce tsarin na kasuwancin na Afirka ba zai shafi harajin cikin gida da aka saba karba a hannun ’yan kasuwa ba, kamar yadda ba zai shafi bangaren kudi na bai-daya ba, in ban da sabuwar takardar kudin kasashen Afirka ta Yamma da za ta fara aiki a lokacin, wanda Najeriya na ciki.

A karshe ya bukaci gwamnati ta yi la’akari da bangaren kwarewa wajen nade-nadenta a dukkan bangarori. Ya ce ba daidai ba ne gwamnati ta nada lauya a matsayin jagora a bangaren wutar lantarki ko aikin hanya da kuma gidaje, maimakon injiniya ko wani mai kwarewa da ke da nasaba da bangaren.