Subscribe
  • facebook
  • twitter
  • whatsapp
  • linkedin
Namiji mafi tsufa a duniya ya rasu

Namiji mafi tsufa a duniya ya rasu

Wani tsoho da aka yi ganin shi ne mafi tsufa a cikin maza a duniya ya rasu yana da shekara 112 a Japan. Rahotanni sun nuna wanda yake rike da kambin tsufar ya rasu ne a farkon makon nan, kamar yadda kafofin labarai a Japan suka ruwaito a ranar Talata.

Chitetsu Watanabe, wanda ya rayu a birnin Joetsu da ke tsakiyar kasar Japan ya rasu a ranar Lahdi, kamar yadda Kamfanin Dillancin Labarai na Japan, Kyodo ya sanar. An haife shi a ranar 5 ga Maris 1907, sai dai kafin rasuwarsa yana zama ne a gidan kula da tsoffi. Ya karbi shaidar mutum namiji da ya fi kowane tsufa a duniya a ranar 12 ga watan Fabrairu daga Kundin Tarihi na Duniya (Guinness World Records).

Bayan ya kammala karatu a makarantar aikin gona, Watanabe ya fita zuwa kasar Taiwan inda ya yi aiki da wani kamfanin sukari na kasar Japan da ke a Taiwan din.

Bayan ya shafe shekara 18 yana aiki a can-daga bisani ya koma kasarsa Japan inda ya shiga aikin soja – lokacin Yakin Duniya na Biyu.

Bayan kare yakin ya sake komawa garin haihuwarsa Niigata, inda ya shiga aikin gwamnati har sai da ya kai shekarun ritaya. Watanabe yana da ’ya’ya biyar da jikoki 12 sai kuma tattaba kunne 17, kamar yadda kafar labarai ta Kyodo ta nuna.

Matar da ta fi kowace mace tsufa a duniya, ita ma tana zaune ne a kasar Japan, sunanta Kane Tanaka. Ta yi bikin cikarta shekara 117 a duniya a watan Janairun da ya gabata. (dpa/NAN)