✕ CLOSE Noma Da Kiwo Hotuna Kiwon Lafiya Girke-Girke Sana'o'i Kimiyya da Kere-Kere Ra'ayin Aminiya Ra’ayoyi Rahoto
Click Here To Listen To Trust Radio Live

Nanfe Joy Jatau: Mai digirin da take wankin motoci

Nanfe Joy Jatau wata matashiya ce da ta kammala karatun digiri a Jami’ar Jos a fannin Wasan Kwakwayo amma ba kamar yadda aka san matan…

Nanfe Joy Jatau wata matashiya ce da ta kammala karatun digiri a Jami’ar Jos a fannin Wasan Kwakwayo amma ba kamar yadda aka san matan Arewa ba, sai ta kama sana’ar wankin mota a garin Jos. A wannan tattaunawa da wakilinmu, ta bayyana yadda ta shiga wannan sana’a da irin nasarorin da ta samu:

 

Yaya aka yi kika kama wannan sana’a ta wankin mota?

To ni dai an haife ni ne a Karamar Hukumar Langtang ta Arewa da ke Jihar Filato. Kuma kafin in kama wannan sana’a bayan da na kammala karatun digirina a fannin Wasan Kwikwayo a Jami’ar Jos, na samu wani aiki a wani kamfanin Inshora a Abuja. Wannan aiki da na samu duk wata ana biyana Naira dubu 20. Shi ne da na ga matsaloli sun yi yawa a Abuja, musamman matsalar tsadar wajen zama sai na ga aikin ba zai yiwu in ci gaba da shi ba, don haka na bari.

Daga nan na dawo Jos na samu aikin koyarwa a wata makaranta a wata ana biyana albashin Naira 5000. Nan ma na ga abin ba zai yiwu ba. Shi ne na samu yayana na ce masa ya taimake ni ya bude mini wajen wanke mota. Ya ce zan iya wannan sana’a? Na ce masa zan iya yi. Shi ne ya ba ni kudi na zo na bude wannan waje, na wanke motoci. Yadda na kama wannan sana’a ke nan. Kuma yanzu na kai shekara daya da kama sana’ar.

Ganin ga shi kin yi karatu har kin yi digiri, ba ki ji nauyin kama wannan sana’a ba?

Ban ji kunya ko nauyin komai ba, tunda ni na sa kaina a wannan sana’a kuma na shiga sana’ar ce domin in samar wa kaina aikin yi. Ai karatu komai zurfinsa wata hanya ce ta inganta rayuwa. Saboda haka don mutum ya yi karatu mai zurfi ko don ya yi digiri ya ce ya fi karfin ya yi wata sana’a musamman a wannan kasa tamu Najeriya da rashin aiki ya yi yawa, ya yaudari kansa.

Babu shakka lokacin da na bude wannan waje, mutane sun yi ta mamakin ganin ni mace amma ga ni na zo ina yin wannan sana’a wadda maza ne aka sani suna yi. Ni dai kawai na ci gaba da wannan sana’a ban damu ba.

Kamar daga wadanne wurare ake kawo miki wankin motoci?

Ina samun wadanda suke kawo mini wanki mota daga nan cikin garin Jos. Kuma kasancewa wannan wuri yana kan hanyar Zariya ne, ina samun ana kawo mini wankin motoci daga wurare daban-daban, kamar Zariya da Kano da Kaduna.

Akalla kina samun kamar nawa a mako?

Akalla a duk mako nakan samu Naira dubu 40, bayan sallamar da nake yi wa yaran da suke taya ni aiki.

Wadanne nasarori kika samu a wannan sana’a?

Babu shakka na samu nasarori masu yawa a wannan sana’a. Domin a yanzu na dauki yara hudu aiki a nan wajen, wadanda nake biyansu. Bayan haka na samu kudi har na sayi fili da zan gina gida nawa na kaina. Sannan ina taimaka wa ’yan uwana da kudade, duk ta dalilin wannan sana’a. Don haka ni a wurina sana’ar wanke motoci ta yi mini daidai.

Mene ne babban burinki a wannan sana’a?

Babban burina shi ne in bunkasa wannan waje ta hanyar bude wurin cin abinci, don idan mutanen da suka kawo mini wanki suka zo, su samu wurin da za su rika cin abinci. Haka kuma ina son in bude wajen gyaran gashi a wannan waje, domin harkoki su dada fadada a wannan waje.

Wane kira kike da shi zuwa ga matasa irinki, wadanda suka kammala karatun jami’a?

Kirana ga matasa musamman wadanda suka yi karatu a jami’a, shi ne su cire girman kai, su kama sana’a, maimakon su tsaya suna neman aikin gwamnati da ba ya samuwa yanzu a Najeriya.