Da Dumi Dumi

Nasarar Buhari a kotu ta ’yan Najeriya ce – MBO

Kungiyar Goyon Bayan Muhammadu Buhari da Osinbajo (MBO) ta Kasa ta ce nasarar da Shugaban Kasa Muhammadu Buhari ya samu a Kotun Zaben Shugaban Kasa, nasara ce ta al’ummar kasar nan baki daya.

Babban Jam’in Kungiyar na Kasa Alhaji Usman Ibrahim ne ya bayyana haka a tattaunawa da wakilinmu a farkon makon nan, inda ya ce hukuncin wani babban abu ne da zai kawo ci gaban kasa da dorewar mulkin dimokuradiyya.

Ya kara da cewa hukuncin ya nuna cewa sashin shari’a na kasar nan ya samu cin gashin kansa a karkashin gwamnatin Buhari.                                                                                                                                                       Alhaji Usman ya yi kira ga ’yan adawa su zo su hada hannu da gwamnatin Buhari don bada gudunmawarsu wajen ci gaban kasar nan da bunkasa mulkin dimokuraddiya. Ya bayyana cewa a tsarin nan na Nes Labul da gwamnatin ta zo da shi, tabbas jama’ar kasa sun fara ganin babban canjin da ake bukata na samun ingattatciyar rayuwa domin ci gabansu.

Alhaji Usman ya ce kamata ya yi duk masu adawa da wannan gwamnati, su rungumi kaddara, domin al’ummar kasar nan sun nuna cewa wannan gwamnati tasu ce kuma su ne suka kada mata kuri’a domin ta dora daga inda ta tsaya a zangon mulkinta na farko. Ibrahim ya ce a bayyane yake cewa zaben da aka gudanar a watan Fabrairun bana, jama’a sun fito kwansu da kwarkwata a kasar nan, suka zabi Shugaban Kasar da suke ganin shi ne mafita ga al’ummar wannan kasa.

Usman ya ce amincewa da kuma yakinin da al’umma suke da su a kan wannan gwamnati ne babban abin da ya sa suka zabenta don ba ta dama dorawa daga inda ta faro a zangon farko, “Don haka wadanda suka gaza samun nasara su bada goyon baya da hadin kansu don a ci gaba da samun zaman lafiya da bunkasar arzikin kasa,” inji shi.

ADVERTISEMENT

 

 

Share
A latsa wannan alamar domin shiga zauren Jaridar Aminiya