✕ CLOSE Noma Da Kiwo Hotuna Kiwon Lafiya Girke-Girke Sana'o'i Kimiyya da Kere-Kere Ra'ayin Aminiya Ra’ayoyi Rahoto
Click Here To Listen To Trust Radio Live

Nasarar Buhari: Wani matashi zai yi tattaki daga Legas zuwa Abuja

Wani Matashi Bashir Rano da ke sana’ar fawa a Legas wanda a halin yanzu yake tattaki a kas daga Legas zuwa Abuja saboda murnar cin…

Wani Matashi Bashir Rano da ke sana’ar fawa a Legas wanda a halin yanzu yake tattaki a kas daga Legas zuwa Abuja saboda murnar cin zaben shugaba Buhari a karo na biyu.

Matashin ya shaida wa Aminiya cewa dalilin da ya sanya yayi tattakin duk da cewa ba shi ne farkon wanda ya fara tattakin ba, yace dalilin yin tattakin shi ne, kafin a yi zabe akwai abokin kasuwancin sa wani dan kabilar Ibo wanda musu ya kaure a tsakanin su, inda shi kabilar ibon yace a yanzu farinjin Shugaba Buhari ya disasa kuma magoya banyan sa sun ragu don haka ba zai ci zabe ba, ba kuma zai samu wadanda zasu yi masa tattaki ba, ” wannan abu da ya faxa sai ya zaburar da ni, nan take nayi rantsuwa cewa muddin Buhari yaci zabe ni kuma zan yi tattaki daga Legas zuwa Abuja a qas domin in tabbatar masa har gobe mu masoya Buhari munanan daram daqam, sai shi kuma yace in dai na yi tattakin shi kuma zai musulum ta, wannan magana da yayi shi ya qarmin qwarin guiwa” inji shi.