Da Dumi Dumi

Nasarar dan siyasa kyautata wa al’umma – Kiyana

Alhaji Sulaiman Jubril Kiyana
Alhaji Sulaiman Jubril Kiyana

Kansila mai wakiltar Obalande a Karamar Hukumar Ikoyi a Jihar Legas Alhaji Sulaiman Jubril Kiyana ya ce, babbar nasarar da duk dan siyasa ba ta wuce kyautata wa al’ummarsa ba, domin suke yin ruwa-da-tsaki su jajirce harya kai ga nasarar don haka duk dan siyasar da ya san abin da yake yi ba zai juya wa al’ummarsa baya ba.

Kansilan wanda shi ne Shugaban Masu Rinjaye na kansilolin yankin kuma daya daga cikin zababbun kansiloli ’yan Arewa hudu ya ce  “Wannan dalili ne ya sa a koyaushe tunanina yaya za a yi in kyautata wa al’umma a, wadanda da jibin goshinsu ne na kai ga wannan matsayi. Kuma burina a matsayina na dan Arewa zababbe in kyautata wa al’umma domin na bayanmu in sun fito  neman takara su samu goyon baya, ta yadda za a ce ai dan Arewa ya yi an ji dadi. Don haka nake dagewa domin mu bar tarihi mai kyau mu yi wa na bayanmun sharar fage, don mu ’yan Arewa da jama’a suka zaba a madafun gwamnatin Legas wata dama ce muka samu don haka dole mu yi amfani da wannan dama domin kyautata wa al’ummarmu.”

Ya ce, yana zama da kansiloli uku ’yan Arewa, biyu a yankin Apapa, daya a Agege inda yake ba su shawarar su hadu su yi hobbasa domin fito da kyakkyawan tsarin shugabanci da ko bayansu in wani dan Arewa ya yunkuro yana neman a zabe shi za a ba shi goyon baya in aka tuna da aikin da suka yi. “Don haka zuwa yanzu na tallafa wa talakawa da gajiyayyu da jari su sama da 200, kuma na taimaka wa marasa lafiya da kudin magani, yanzu ina shirin tallafa wa mata da yaran da ke zaune a barikokin soji mata za mu ba matansu da matasa 100 tallafi. Wannan taimako ne na mazauna bariki kadai na fito da wannan tsari ne don kyautata alakarmu da su da kara sada zumunci a tsakanin matan soji da na ’yan sanda, domin mun lura wannan yankin na jama’a suna kokawa cewa, an bar su a baya. Don haka ya sa ba ma samun kuri’un kirki daga gare su a lokacin zabe, don haka tilas mu kyautata alakarmu da su, mu tallafa musu don su samu romon dimokuradiyya,” inji shi.

Ya ce baya ga su za su ba mata ’yan kasuwa tallafi tare da matasa masu  acaba.

Ya ce tallafin zai fara ne ta kan al’ummar da ke zaune a barikin soji da ’yan sanda da ke Obalende a ranar 1 ga Oktoba yayin da ragowar tallafin za su biyo baya duk a watan.

ADVERTISEMENT

Sai ya yi kira ga ’yan uwansa ’yan siyasa su yi amfani da damar da Allah Ya ba su wajen kyautata wa al’ummarsu domin ta haka ne za su samu tsira da tarin lada a wajen Ubangiji.

Share