✕ CLOSE Noma Da Kiwo Hotuna Kiwon Lafiya Girke-Girke Sana'o'i Kimiyya da Kere-Kere Ra'ayin Aminiya Ra’ayoyi Rahoto
Click Here To Listen To Trust Radio Live

Nasarar El-Rufa’i nasarar dimokuradiyya ce – Sarkin Samari Daga Ahmed Ali, Kafanchan

Sarkin Samarin Jama’a da ke Jihar Kaduna Alhaji Mudi Shafi’u Tahir ya bayyana nasarar da Gwamnan Jihar, Malam Nasir Ahmad El-Rufa’i ya samu a shari’arsa…

Sarkin Samarin Jama’a da ke Jihar Kaduna Alhaji Mudi Shafi’u Tahir ya bayyana nasarar da Gwamnan Jihar, Malam Nasir Ahmad El-Rufa’i ya samu a shari’arsa da dan takarar Gwamnan Jihar na Jam’iyyar PDP a zaben bana, Alhaji Isa Ashiru Kudan cewa nasar ce ga dimokuradiyya.

Sarkin Samarin, ya ce nasarar Gwamna El-Rufa’i kuri’un da Gwamnan ya samu daga kowace shiyya ta jihar tare da gagarumin rinjaye kan abokin takararsa a jihar da ta yi kaurin suna wurin zafafa siyasar addini da kabilanci, alama ce da ke nuna wayewar al’umma da irin ci gaban da aka samu a dimokuradiyya.

“An gudanar da zabe lafiya cikin kwanciyar hankali tare da sa idon masu lura da ingancin zabe kuma babu wani korafin a zo a gani a kai,” inji shi

Sarkin Samarin, wanda ya bayyana haka Aminiya kan nasarar da kotu ta tabbatar wa El-Rufa’i, ya ce bayan fatar  alheri ga Gwamnan da addu’ar samun nasara a wa’adi na biyu, ya yi kira ga Gwamnan  da ’yan majalisarsa su hada kai wajen ganin sun aiwatar da ayyukan raya jihar tare da samar da walwala da jin dadi ga al’umma wanda hakan zai dada karfafa zaman lafiya da fahimtar juna a tsakanin shiyyoyin jihar.

“Muna rokon Gwamna El-Rufa’i bisa kyawawan kudirori da manufofinsa, ya tuna da alkawuran da ya yi lokacin yakin zabe d sauran hakkoki da ke wuyan shugaba ko da bai yi alkawari ba, ya saurari koke-koken jama’a don magance wadanda zain iya,” inji shi.