Search
Subscribe
Nasarar yaki da cutar COVID-19 nasara ce ta duniya

Nasarar yaki da cutar COVID-19 nasara ce ta duniya

A daidai lokacin da wakilan Hukumar Lafiya ta Duniya (WHO) suka ce kasar China tana kokari sosai wajen dakile yaduwar cutar Kurona (COVID19), Malam Ibrahim Yaya (Imail:iyayag@yahoo.ca) na Sashin Hausa na Rediyon China a Beijing ya yi sharhi kan halin da ake ciki game da wannan cuta da ta zama barazana ga duniya:

Tun lokacin da mahukuntan kasar China (Sin) suka sanar da bullar cutar Kurona COBID-19 a birnin Wuhan da ke Lardin Hubei, gwamnatin birnin ta bayyana rufe filin saukar jiragen sama da tashar jiragen kasa ta birnin, kuma aka dakatar da dukkan hanyoyin sufuri zuwa wani lokaci, kuma aka bukaci mazauna birnin kowa ya zauna a gida. Wannan wani muhimmin matakin kandagarki ne da ya dace gwamnatin kasar China ta dauka domin dakile yaduwar cutar da kuma kiyaye lafiyar al’umma baki daya da tabbatar da tsaron lafiya jama’a a daukacin duniya.

Wannan ba shi ne karon farko da kasashe daban-daban suke daukar irin wannan mataki na kandagarki ba domin shawo kan yaduwar cututtuka a tarihin dan Adam. Alal misali, a shekarar 2014, domin hana yaduwar cutar Ebola, wasu kasashen Afirka ciki har da Guinea da Saliyo da kuma Laberiya sun sanar da kafa wani kebabben wuri a bakin iyakokinsu.

Babban Daraktan Kungiyar Lafiya ta Duniya (WHO) Tedros Adhanom Ghebreyesus ya ce, matakan da gwamnatin China ta dauka sun dace matuka, kuma a ganinsa yana da muhimmanci da gwamnatin ta dauki wadannan matakai da suka dace da hakikanin halin da ake ciki.

Gwamnatin China ta dauki matakan kandagarkin yaduwar cutar ba tare da bata lokaci ko wata rufa-rufa ba, al’amarin da ya nuna cewa kasar na tana sauke nauyin da ke kanta ga duniya, duk da cewa wasu kasashe sun nuna kyama ga mutanen China, suna kokarin hana su shiga kasashensu, ko nuna musu kyama da wariya.

Yauzu haka daukacin al’ummar China sun zama tsintsiya madaurinki daya domin yaki da wannan annoba. Kuma managartan matakan dakile yaduwar cutar da kasar ke dauka, sun samu amincewa da goyon-baya daga kasashe da dama.

Abin takaici shi ne, duk da irin wadannan matakai da nasarori da ake samu na ganin bayan wannan annoba, akwai kafofin watsa labaran kasashen Yamma da suka ce China ta kambama yanayin da ake ciki ta hanyar daukar matakan da suka wuce gona-da-iri, har ta kai ga keta hakkokin dan Adam.

Wannan zargi da aka yi wa China ba gaskiya ba ne, kuma babu tausayi cikinsa ko kadan, kawai wasu kasashen Yamma ne ke son shafa wa kasar kashin kaji ta fakewa da kare hakkin dan Adam. Sannin kowa ne cewa, annoba ba ta da iyakar kasa, ma’ana tana iya shafar kowace kasa.

Wani muhimmin mataki da gwamnatin China ta dauka don ganin bayan cutar shi ne gina asibitocin kula da wadanda suka kamu da cutar cikin kwana 10 kacal a Huo Shenshan da Lei Shenshan masu gadaje 1000 da 1600, baya ga dimbin asibitocin wucin-gadi da aka samar da gadaje dubu 10. Kuma an tura ma’aikatan lafiya sama da dubu 30 zuwa Lardin Hubei don yaki da cutar.

Abin bakin ciki da takaici, duk da nasarorin da kasar China ta cimma kan yaki da annobar a kwanan nan, jaridar New York Times ta wallafa wani bayani mai taken “SARS da murar tsuntsaye da cutar Kurona: Me ya sa cututtuka masu yaduwa da dama suka barke a China?” Rahoton ya ruwaito Peter Nabarro, Shugaban Kwamitin Harkokin Cinikayya na Amurka yana bayyana China a matsayin ‘na’urar kyankyasar cututtuka.’

To, amma abin tambaya, me ya sa cutar mura da ake kira ‘Spanish flu’ da ta hallaka mutum miliyan 50 a farkon karnin da ya gabata ta fara bulla a wani sansanin soja da ke Jihar Kansas ta kasar Amurka? Sai kuma a shekarar 2009, cutar murar tsuntsaye nau’in H1N1 ta barke a Amurka, har ta yadu zuwa kasashe da shiyyoyi 214, inda daga baya ta harbi mutum miliyan 60 a fadin duniya, kuma dubu 300 daga cikinsu suka mutu. A bara murar Influenza B ta bulla a sassan Amurka, har rahoton da cibiyar rigakafin cututtuka ta Amurka ta ba da ya nuna cewa akalla sama da mutum miliyan 22 suka kamu da cutar, daga cikinsu dubu 12 sun mutu. Cututtuka makiya dan Adam ne baki daya, babu wata kasa ko wata al’ummar da za ta iya tsira daga gare su.

A yayin da kasashen duniya ke kara dunkulewa da zarar China ta shawo kan cutar, tabbas harkokin cinikayya da zirga-zirga za su farfado a duniya, kuma hasarar da kasashen duniya suka tafka sanadiyar cutar za ta ragu. Nasarar kawar da cutar nasara ce ga duniya baki daya. Yanzu haka, al’amura sun fara farfadowa a sassan kasar China. A yayin da ayarin kwararrun da Hukumar WHO ta tura ya sauka a birnin Beijing, jiragen kasa na dakon kayayyaki dauke da manyan kwantainonin kaya 41 sun tashi daga birnin Zhengzhou na Lardin Henan zuwa yankin tsakiyar Asiya, abin da ke nuna cewa, an dawo da zirga-zirgar jiragen kasa a tsakanin China da Turai, wanda hakan ke nuna cewa, China tana kokarin kiyaye jama’arta da al’ummomin duniya baki daya.

Wannan na nuna cewa, makarkashiyar wasu kasashe ta mayar da China saniyar ware ba za ta yi nasara ba, kuma hakan ya saba wa burin al’ummomin duniya, da suke ganin in aka hada kai, aka yi watsi da nuna kiyayya za a ga bayan wannan annoba cikin kankanen lokaci.

Wani abin haushi kuma shi ne wadansu mutane da kafofin watsa labarai na Yamma suna zargin cewa kasar China ce ta samar da kwayar cutar COBID-19 a shirinta na ‘makamai masu guba,’ suna zargin cewa, kwayar cutar, ta fito ce daga dakin gwaje-gwajen makamai masu guba.

Wane mutum mai hankali ne zai kirkiro cutar da za ta hallaka gidansa? Kafofin watsa labaran suna baza jita-jita marasa tushe ne don shafa wa China kashin kaji, bisa rashin sani ko ganganci.

Jami’an Hukumar WHO sun sha bayyana cewa, babu shaida ko kadan da ta nuna cewa kwayar cutar numfashi ta COVID-19 ta fito ce daga dakin gwaje-gwaje, ko na makami mai guba da China ta samar. Kuma fitattun likitoci da dama a kasashe daban-daban suna ganin cewa, jita-jitar da aka baza kan batun ba su da tushe a bangaren kimiyya

Wani labari mai dadi shi ne, a ranar 10 ga Fabrairun nan, kamfanonin China sun fara komawa bakin aiki sannu a hankali sakamakon samun nasarar yaki da cutar. A halin yanzu ban da Lardin Hubei, kamfanoni a larduna da birane 30 na kasar China sun fara aiki. Bayanai sun ce, gwamnatin tsakiya ta da gwamnatocin yankunan China sun rage kudin da ake kashewa kan tattara kudi da ba da rangwamen haraji da tabbatar da ayyukan jama’a da sauransu don samar da yanayi mai kyau na farfado da ayyukan kamfanonin.

Babu shakka China ta sa duniya ta fahimci cewa, hadin gwiwa da imani sun fi komai daraja. A wannan zamani da duniya ke kokarin dunkulewa wuri daya, babu wata kasa da za ta iya tunkarar wata matsala ita kadai. Jama’ar China ba za su manta da goyon baya da taimakon da kasashen duniya ke ba su ba. Annobar za ta wuce, hadin gwiwar da aka samu lokacin da aka fuskanci matsalar za ta kara samar da sabuwar dama ta inganta hadin kai a nan gaba.

Shugaban Kasar China, Mista Di Jinping, ya ba da umarnin cewa, ya zama dole a maida hankali kan cikakkiyar kula da kariya ga ma’aikatan jinya, don tabbatar da suna aiwatar da ayyukansu lami-lafiya. Zuwa ranar 13 ga Fabrairu, hukumomin China sun ware Yuan biliyan 25.94, don sayen kayan jinya da na kariya iri-iri da kyautata na’urorin aikin jinya a asibitoci. Fata nagari lamiri. Allah Ya kawo mana saukin wannan annoba, amin.

  • facebook
  • twitter
  • whatsapp
  • linkedin