✕ CLOSE Noma Da Kiwo Hotuna Kiwon Lafiya Girke-Girke Sana'o'i Kimiyya da Kere-Kere Ra'ayin Aminiya Ra’ayoyi Rahoto
Click Here To Listen To Trust Radio Live

Nasarawa ta yi tsarin inganta ilimi a cikin shekara hudu

Jihar Nasarawa ta kaddamar da shirin inganta ilimi cikin shekara hudu. Kwamishinar Ilimi ta Jihar, Hajiya Fatu Sabo ce ta fadi haka a Lafiya yayin…

Jihar Nasarawa ta kaddamar da shirin inganta ilimi cikin shekara hudu.

Kwamishinar Ilimi ta Jihar, Hajiya Fatu Sabo ce ta fadi haka a Lafiya yayin bude taron sanin makamar aiki na wuni biyar da aka shirya wa daraktoci da manyan ma’aikata don ganin an cimma burin da aka sa a gaba.

Ta cewa, gwamnati tana da burin ganin jihar ta zama ta uku a kasar nan a tsakanin jihohin da suka bunkasa a shekaru kadan nan gaba.

Hajiya Fatu Sabo ta ce, “Tsarin bunkasa ilimn zai yi la’akari ne da samar da ilimi musamman ga ’yan mata don a kawar da su daga tallace-tallace a kan tituna.”

Ta kara da cewa, an kudiri aniyar bunkasa samar da ilimin sana’o’i da kere-kere don tabbatar da cewa dalibai sun zamo masu dogaro da kansu bayan sun kammala makaranta. Kuma  za a kara gina sabbabin ajujuwa da yin kwaskarima ga wasu.

Kwamishinar ta ce duk da an kebe kashi 26 na kasafin kudin bana ga ilimi, sashin yana bukatar tallafi.

A jawabin wata masaniya kan harkokin ilimi, Hajiya Jummai Sarki, ta ce suna da burin samar da ma’aikatar yadda ake koyo da koyar da jagorancin ilimi ga na baya kamar yadda aka yi a sauran jihohi.