✕ CLOSE Noma Da Kiwo Hotuna Kiwon Lafiya Girke-Girke Sana'o'i Kimiyya da Kere-Kere Ra'ayin Aminiya Ra’ayoyi Rahoto
Click Here To Listen To Trust Radio Live

Nasarawa United ta sallami kocinta da wasu ’yan wasa

Hukumar gudanarwar kungiyar kwallon kafa ta Nasarawa United a Jihar Nasarawa ta bayyana kudirinta na daidaita kungiyar domin yin abin kirki a  kakar wasanni mai…

 Gwamnan Jihar Nasarawa Umaru Tanko Al-makuraHukumar gudanarwar kungiyar kwallon kafa ta Nasarawa United a Jihar Nasarawa ta bayyana kudirinta na daidaita kungiyar domin yin abin kirki a  kakar wasanni mai zuwa.
Haka kuma hukumar  ta ce tuni ta sanya ’yan kwallon Nasarawa United su 13 a kasuwa yayin da ta sallami guda 27.
Hukumar ta ce ta dauki wannan matakin ne bayan yin nazari a kan ‘yan wasan a kakar wasan kwallon da ta wuce.
Hukumar ta ce tuni ta ba da aron ‘yan wasa hudu ga wasu kungiyoyin kwallon kafa yayin da ta gargadi ‘yan kwallo biyu don ganin sun zage damtse a kakar wasa mai zuwa.
 Ahalin da ake ciki, an sallami tsohon kocin kungiyar wato Mista Silbester Ikojo kamar yadda aka sallami mai horar da mai tsaron gida Mike Jathau.
A sakamakon haka ne aka nada kocin karamar kungiyar Nasarawa United Abubakar Arikya a matsayin babban kocin kungiyar yayin da Khadiri Ikhana zai cigaba da rike mukamin mai ba kungiyar shawara.