Da Dumi Dumi
ADVERTISEMENT

Nasiha ga iyayen da ke barin tarbiyyar ’ya’yansu a wajen wasu (3)

Nasiha ga iyayen da ke barin tarbiyyar ’ya’yansu a wajen wasu (3)

Akwai lokacin da Amira ta dawo daga makaranta amma Zuwaira ta hana ta abinci. Hasali ma kanzo ta zuba mata kuma ta umarci Amira ta cinye ko ta kashe ta.  Haka Amira ta rika ci saboda yunwa da tsoron kada Zuwaira ta kashe ta.

Haka aka yi ta tafiya babu wanda ya san abin da ke faruwa tsakanin Zuwaira da Amira.

ADVERTISEMENT

Akwai lokacin da Hassana uwar Amira ta samu gajeren hutu ta kasance a gida sai ta fahimci dabi’un Amira sun canja.  Da ta duba sai ta ga kamar jikin Amira  ya yi rudu-rudu kamar an doke ta.  Ta nemi jin yadda aka yi sai Amira ta fara kuka gudun kada ta fada Zuwaira ta kashe ta.  Ana cikin haka ne sai Zuwaira ta shiga falon da Hassana ke zaune da Amira, nan take Hassana ta nemi jin abin da ya faru da Amira, inda ita kuma ta yi karyar Amira ta taba zamewa ne ta fadi a lokacin da take kokarin shiga ban-daki.  Nan take Amira ta nuna haka ne, bayan Zuwaira ta harare ta, haka dai magana ta wuce.

Bayan kwana biyu sai Zuwaira ta koya wa Amira sata, inda take umartarta ta sato mata kudi a dakin Hassana.  Abin na damun Hassana, domin duk lokacin da ta ajiye jakarta a cikin dakinta, takan lura ana taba mata kudi ba tare da sanin wanda yake aikata haka ba. Ashe da zarar ta koma gida ta ajiye jakarta ta shiga wanka, sai Amira ta lallaba ta dumbuzo kudi ta kai wa Zuwaira, ita kuma take kai wa saurayinta ba tare da sanin kowa ba.

ADVERTISEMENT

Kafin lokaci kankane sai Amira ta kware wajen satar wa Hassana kudi tana mika su ga Zuwaira.  Hassana ta sanar da mijinta Kabiru halin da ake ciki, kuma ta nuna mamakin yadda hakan ke faruwa don ba mai shiga bangarenta in ban da mijinta Kabiru sai kuma ’yarsu Amira.  Kuma yadda take daukar Amira karamar yarinya a zatonta ba za ta iya aikata haka ba.

Ran nan sai ta dana tarko.  Bayan Hassan ta koma gida sai ta yi kamar ta shiga wanka sai ta labe ne a bayan kofa. Ba a jima ba sai ga Amira ta lallabo cikin dakin ta zura hannu a cikin jaka ta dumbuzo kudi.  Dibowarta ke da wuya sai Hassana ta yi salati, ta ce “Amira!” Da ma ke ce kike yi mini sata.  Nan take Amira ta fara kuka tana nuna waje.

Mu kwana nan

 

Za a iya samun Ahmed Garba Mohammed a 08028797883