✕ CLOSE Noma Da Kiwo Hotuna Kiwon Lafiya Girke-Girke Sana'o'i Kimiyya da Kere-Kere Ra'ayin Aminiya Ra’ayoyi Rahoto
Click Here To Listen To Trust Radio Live

Nasiha ga iyayen da ke barin tarbiyyar ’ya’yansu a wajen wasu

Masu bibiyar wannan shafi na Iyayen Giji ina yi muku sallama irin ta addinin Musulunci, assalamu alaikum. Barkanmu da sake haduwa a wannan fili da…

Masu bibiyar wannan shafi na Iyayen Giji ina yi muku sallama irin ta addinin Musulunci, assalamu alaikum. Barkanmu da sake haduwa a wannan fili da muke fadakar da juna a kan al’amura daban-daban musamman wadanda suka shafi zamantakewar aure. Muna jin dadin yadda masu karantu wannan shafi suke turo sakonnin gyara ko na yabo game da abubuwan da muke kawowa don mu yi nazari a kansu, domin mu gudu tare mu tsira tare.

Kwana biyu ban yi rubutu a wannan shafi ba saboda hutun da na yi, amma yanzu na insha Allah za mu ci gaba da fadakar da kanmu kan abubuwan da suka shafe mu.

Yau zan kawo wani labari ne da yake ci mana tuwo a kwarya. Labarin ya faru ko in ce yana faruwa a kullum musamman a gidajen aure, yadda za ka ga wadansu iyaye saboda wasu dalilai na kashin kai suna barin tarbiyyar ’ya’yansu a wajen wadansu, musamman ’yan aikin gida inda daga karshe hakan ke haifar da matsala.  Hakan na faruwa a gidajen aure daban-daban kamar yadda wannan labari ya nuna, inda wadansu iyaye suka shiga cikin damuwa bayan sun bar tarbiyyar ’yarsu a wajen wata ’yar aikin gida.  Ba su tashi ankara ba har sai da ’yar aikin ta yi musu illa. Don haka wannan labari ina fata zai zama darasi ga iyayen da ke aikata haka ko neman aikata irin wannan dabi’a.

Ga yadda labarin ya kasance:

A wani gari ne da ke nan Arewa (an sakaya sunan garin), an yi wadansu ma’aurata biyu Kabiru da Hassana (ba sunansu na ainihi ba). Dukkansu suna da rufin asiri daidai gwargwado. Kabiru kwararren likita ne, yana aiki da asibitoci masu zaman kansu da dama. Hakan ya sa ba ya da isasshen lokaci na kashin kansa, domin a kullum yana zirga-zirga ne a tsakanin asibitocin don duba marasa lafiya.  Idan Kabiru ya bar gida tunda sassafe, kafin ya koma sai tsakar dare, wani lokacin ma a can yake kwana sai dai ya sanar da matarsa Hassana halin da yake ciki.

Hassana kuwa, ma’aikaciyar banki ce,  ta kware a harkar banki, a dalilin haka ne ma suka hadu da Kabiru (mijinta) lokacin da ya ke bankinsu don ajiyar kudi.  Hakan ya janyo suka kulla soyayya har suka yi aure.

Allah Ya albarkace su da haihuwar ’ya mace da suka sanya wa suna Amira. Amira ta kasance tamkar gwal a wurin Kabiru da Hassana saboda irin soyayyar da suke nuna mata.

Kwanci-tashi har Amira ta kai shekara biyar inda suka yanke shawarar sanya ta a makarantar boko da ta addini.

Sai dai kash saboda yadda ma’auratan ba su da isasshen lokaci, sai suka yanke shawarar daukar ’yar aikin gida da za ta rika kula da Amira a lokaci guda kuma tana kula musu da gida, musamman ganin dukkansu ba mai komawa gida da wuri.

Ma’auratan sun bar alhakin kula da gidansu ga wata ’yar aikin gida ce da ake kira Zuwaira.

Zuwaira ita ke dafa musu abinci da safe sannan ita ke kula da Amira idan ta koma gida daga makaranta, sannan ita ke kula da dukkan dawainiyar gida da suka hada da shara da wanke-wanke da goge-goge da kuma zuwa kasuwa don yin cefane da sauransu.

Mu kwana nan

 

Za a iya samun Ahmed Garba Mohammed a 08028797883