Da Dumi Dumi

Nasiha ga matan da ba su samu mijin aure da wuri ba

Assalamu alaikum Editan jaridarmu mai tarin albarka wato Aminiya. Don Allah ka ba ni dama in dan yi fashin baki dangane da zaman rashin miji da  wadansu mata ke yi a gidajensu,

Sau da yawa za ka samu mace ta kai wani mataki wanda ya kamata a ce ta yi aure amma ba ta yi ba, sa’o’inta duk sun yi aure wadansu ma har da ’ya’ya ita kuma rashin yin auren ba daga gare ta ba ne, tana so, amma Allah bai kawo mata mijin aure ba.

’Yar uwa, wannan ba komai ba ne illa jarrabawa daga Allah Mabuwayi. Mai yiwuwa Ya jarrabe ki ne domin Ya ga yadda za ki yi, idan kika yi hakuri kuma kika mayar da al’amuranki ga Allah, sai ki ga Ya kawo miki miji adali mai addini da kyawawan dabi’u da dukkan siffofin da mace za ta bukata a wajen namiji ta hanyar da ba ki yi tsammani ba.

Allah Shi ne Ya yi alkawarin zai jarrabi muminai a duniya da jarrabawa iri-iri, kuma Ya ce lallai a yi bushara ga masu hakuri.

’Yar uwa wani irin babban rabo kike tunani Allah Ya tanadar miki idan kika kasance cikin masu hakuri.

ADVERTISEMENT

Hakurin shi ne a kowane lokaci ki rika jin Allah Yana sonki, kuma Yana sane da halin da kike ciki, kada ki kai kukanSa wajen bayinSa, kuma ki kasance mai kiyaye iyakokinSa, ki tsare ganinki da jinki daga haram kuma ki kiyaye al’aurarki, ki kare mutuncin kanki kuma kada ki tozartar da tarbiyyar da su abba da umma suka ba ki. Kada ki aikata abin da za su yi da-na-sanin zuwanki duniya, Sannan kada ki aikata abin da zai zama abin gorantawa ga kannenki da ’ya’yanki da duk wanda yake da alaka ta jini da ke!

Ki bar tarihi mai kyau ko don gaba, kuma ki ji tsoron Allah, ki rika yin dubi ga abin da kike aikatawa don gobe.

Da yawa daga cikin ’yan mata kamilallu sun rasa kimarsu, inda suke tunanin mai yiwuwa sanya wadataccen hijabi da nikabi ne ya jawo masu jinkirin aure, sai suka koma yin shiga irin ta tsiraici da bayyana adonsu wai da sunan samun mijin aure.

’Yar uwa wallahi arahar ta yi yawa, me ya sa sai kin tallata kanki za ki samu miji?  Kin taba ganin wani abu mai daraja ana tallata shi, duk wani abu mai daraja rufe shi ake kuma a adana shi a mafi dacewar wuri, shin a tunaninki tsinuwar Allah da ta mala’iku su za su yi miki jagoranci wajen neman mijin aure? Ki watsar da wannan mugun tunani ’yar uwa.

Ki killace kanki, ki dauki kanki tamkar sarauniya, Allah Masani ne a kan halin da kike ciki, kuma Shi zai turo miki miji nagari, domin su mata masu tarbiyya na maza masu tarbiyya ne, su kuwa lalatattu sai lalatattu irinsu.

Mata nawa ne suka yi aure amma har yanzu ba su shaida dadinsa ba? Nawa ne suka rabu da iyayensu suka je gidan wani amma ya rika azabtar da su, wata ma sai ta gwammace da ma ba a haife ta ba.

Ashe  ke nan yin auren ba shi ke tabbatar da natsuwa ba, sai an bi hanyar da Allah da ManzonSa (SAW) suka tsara.

Ku kuma masu tsangwamar irin wadannan mata da cewa sun ki yin aure, ku ji tsoron Allah ku daina, ku sani kowa akwai irin kaddararsa a rayuwa.

Sai ka ji an zauna ana hirar wance ga kannenta sun yi aure har da yara, amma ita ta ki yin aure.

Wallahi ku sani ta fi kowa son ta yi auren, kuma iyayenta ma sun kosa su rabu da ita amma yaya za su yi tunda haka Allah Ya tsara?

Za a iya samun Nura Sani Rijau a 08108291641

Whatspp 08026664213

 

Tura
A latsa wannan alamar domin shiga zauren Jaridar Aminiya